TAMBAYA GA DAN NIGERIA
MEYA FARU A ZARIA RANAR 12 13 14 -12 -2015??
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq
Aranar sha biyu ga watan disamban shekara da dubu biyu da sha biyar 12-12- 2015 Wanda yayi dai-dai da 1-3-1437H Yan Uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Yaqoub Alzakzaky sun taro a Muhallin Hussainiyya Zaria domin Halattar Bikin sanya tutar Maulidi a wannan ranar ta daya ga watan Maulidi tun misalin karfe goma na safe har zuwa karfe shadaya 11:00ns lafia lau anata shirye-shirye inda adaidai wannan lokaci ne Mahalarta wannan taro sukaga ayarin Sojoji bataliya daya sun zo sun yada zango avakin gidan man NNPC dake setin Hussainiyya Baqiyatullah Zaria a inda suka nemi jin tabakin wadannan Sojoji ta hanyar yi musu tambaya da cewa ko-me sukeyi anan ganin basu saba yin irin wannan ba? Se suka ansa da cewa wai Suna tsaye anan ne saboda akwai bukin saye sabobin Sojoji da za'ayi kuma shugabansu ze wuce ta nan -
jin wannan ansar be gamsar da Mahalarta wannan wuri ba se suka mayar musu da magana ta hanyar tambayar cewa ai ba wannan lokaci ne na farko ba da kukayi irin wannan taro na yaye Sababbin sojoji ba (passing out) Dan haka ba bukatar tsayawarku anan, sedai idan kunzo da Wata manufa ne?
-----
Bayan wannan Dan musayar maganganu tsakanin wadannan Bayin Allah Raunana wadanda basa rike da Wani makami da wadannan Sojoji masu dauke da manyan makamai Bindigogi da bomb da tankokin yaki da sauransu kawai se sojojin nan sukayi Wani yunkuri kamar zasu tafi sukaja da baya kadan kawai se suka Bude musu wuta kai kace dama sun tsara yin wannan mummunan aika-aika yayin nan take mutum bakwai 7 daga cikin wadannan Bayin Allah Raunana suka Riga mu gidan gaskiya,
----
Wannan atakaice kenan abinda yafaru kafin zuwan tawagar Shugaban na Sojoji da ake jinkina wannan Mummunar ta'asar da cewa Wai antare masa hanya ne yayinda yazo wuce ta wannan Muhalli, Wanda Sam abun ba haka yake ba domin kuwa wadannan Bayin Allah sun nema jin tabakin Shugaban wadannan Sojoji ne domin sanin meyasa akayi musu wannan rashin Adalchi amma me makon samun sauki se qarin zalunci daga garesa Dan kuwa be saurare su ba! Sema Wani Uzuri da yake basu cewa yana Uzuri yanzu amma ze saurari kokensu daga baya Wanda wanne yasa sukace bazai yiwu ba inda har takai ga su sojojin sun sake bude wuta akaro na biyu da zummar wucewa da karfin tsiya tunda Shugabansu yace bazai Saurari kojen Bayin Allah Raunana ba su kuma Raunanan Suna kokarin ganin an saurare su din..
.
------
MEYA HAU KAN-MU MU JAMA'AR GARI BISA WANNAN LAMARI?
.
mu namu shine yi musu dukkan abinda zamu iya na adalchi da tausayi gwargwadon iyawarmu domin kuwa wadannan Bayin Mazlumai ne kuma Addinin mu ya koyar damu tausayawa Wanda aka zalunta koda kuwa ba Addinin mu daya dashi ba, ina-ce Manzon Rahama (SAW) shine abin koyin mu kamar yanda yazo acikin Alqur'ani me tsarki Allah Ta'ala asuratul Ahzab yana cewa:-
WALLAHI HAKIQA GAREKU YA TABBATA ABIN KOYI RUSULLAHI (S) ME KYAU IDAN KUNA SON SAMUN SAKAMAKO ME KYAU GOBE QIYAMA KUMA KUNA TSORON UQUBA ARANAR QIYAMA, MANZON RAHAMA KENAN
,,,
saboda haka be zai yiwu ba mu goyi bayan zalunci alhali muna bukatar tamu tayi kyau gobe QIYAMA kuma gashi tun farko muna raya cewa mun yadda munyi Imani da Qur'ani Wanda mungani acikin Allah yace ya Hanawa kansa zalunci kuma ya sanyishi abun haramtawa tsakanin bayinsa bece tsakanin Musulmi kawai ba, wannan ze iya yiwuwa har dabbobi kenan Dan su Kansu Bayinsa ne bare kuma Mutane dukansu, da wannan nake cewa yazan wajibi garemu mu kaucewa zalunci da duk iyawarmu ko zamu samu Uzuri wajen Allah gobe QIYAMA Dan kuwa wadannan Bayin Allah Yan Uwa Musulmi Almajiran Malam Zakzaky H an zalunce su ne maganar gaskiya kuma bamuda Uzuri akan goyan bayan wadanda sukayi wannan Zalunci..
-----
KO KASAN HAR GOBE ANA CIGABA DA ZALUNTAR SU KUWA?
.
tun farkon faruwar wannan lamari Mara dadin ji inda ya soma awannan Muhalli nasu wato Hussainiyya Zaria inda nan ne Malamin nasu yake gabatar da karatuka da wasu bukukuwa wadanda sukeyi,, lamarin ya cigaba har zuwa gidan Malamin Nasu inda acan gidan nasa ne akafi asarar rayuwa masu yawa Wanda Alkalumansu abakin Wadannan Raunana sun haura dubu 1000+, abakin gwanbati 347 kafin daga bisani akama Shehin Malamin nasu Wanda har kwanan gobe Ana tsare dashi duda cewa babbar kotun Kasa ta bada Umarnin Sakinsa tun shekarar bara..
Wannan ne yaqara fito da zaluncin Sojan Nigeria fili domin kuwa kotunsu ce ta tabbatar bashida laifi har tace asake shi amma kuma anyi kunnen Uwar shegu da batun kotun, kaga kenan har gobe ana cigaba da zaluntarsu tunda dai kotu ma ta tabbatar basuda laifi kuma ta Umarci wadanda suka tsareshi da cewa su sakeshi kawai bashida laifi..
--
Zan takaita anan kasancewar Alkalamina bazai iya bayyana dukan abibda yafaru ba!!!
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Sokoto
08132933333
Tags:
#FREE_ZAKZAKY