Tun daga kan manzon farko wato Annabi Nuhu (a.s) zuwa kan manzon karshe Annabi muhammad(s.a.w)da kuma salihan bayi da Allah yake tayarwa lokaci bayan lokaci shin akwai wani wanda mahukumtan zamaninsa sukayi maraba da shi?
In muka dauki Annabi Nuhu shekararsa dubu ba hamsin yana da'awar jama'a su kadaita Allah amma ina kullum sai sunyi yunkurin kashe shi.
Annabi Ibrahim(a.s)shima haka ta kasance a gare shi,inda suka yanke shawarar a jefa shi wuta ya kone
Annabi musah(a.s)shima bai sha dadi shi da jama'arsa wajen fir'auna ba,karshe sai da aka yanke masa hukumchin kisa shi da jama'arsa suka gudu suka bar gari daga nan Allah ya taimake su.
Annabi Isah(a.s)al'ummarsa ta hada meeting da na kusa da shi ta yadda za a kama shi a kashe Allah ya kubutar da shi zuwa sama.
Annabi Muhammad(s.a.w)Bayan sun kira shi Al,Amin,amma da yaxo masu da sakon Allah sai suka karyata shi suka shirya kashe shi baki daya,cikin dare Allah ya umurce shi ya bar garin makka.
Ko da yabar garin na makka sun bishi da yaki tsawon shekara Ashirin da biyar har Allah ya cika alkawarinsa a kanshi da muminai.
TO DON ALLAH SHIN ALLAH BAYA SON SUNE?
Tags:
Muhimman zantuka