WANNAN ABU DA MI YAYI KAMA?===TALAKKAN NAJERIYA KAYI TA KANKA KASHI NA BIYU (2)


A Jiyane assabar na saurari wani rahoto a BBC Hausa inda aka ruwaito cewa gwamnatin najeriya ta amince zata kashe naira biliyan talatin da bakwai (37bn) domin gyaran majalissar kasa. Bana daga cikin masu kwatanta wannan aikin gyara da kuma kasafin kudin wasu ma'aikatu kamar ilimi, lafiya, hanyoyi, domin su aiki ne na shekara daya, shi kuma gyaran majalissa idan anyi shi zai dauki tsawon lokaci.

To amma magana ta gaskiya wannan kudi da akasa sun nuna cewa shugabanin kasar nan basu tunanin talakka, ya jama'a kunsan biliyan daya kuwa?? Itace miliyan dubu daya, wato kenan miliyan dubu talatin da bakwai za'a kashe domin gyaran majalissar kasa.


Bari in kara fiddo da mi ake nufi da biliyan daya, domin irin mu, mutanen karkara su fahimci abin sosai, 1,000,000,000 ÷360 ÷130 =# 21,367. Wato abin da lissafin nan yake nunawa idan aka ba mutum daya naira biliyan daya, zaiyi shekara Dari da talatin yana kashe dubu ashirin da daya da Dari uku da sittin da bakwai, a kowace rana kafin kudin su kare.

To irin wannan kudin sune har biliyan talatin da bakwai aka ware domin gyaran gini, bawai sabon gini ba. Kuma shin wai minene dalilin gyaran? zama ne fa kawai ake ayi zance a tashi, kuma wajan ba kudin shiga yake samarwa najeriya ba, sannan rashin gyaran ba hana aikinsu zaiyi ba. Na tabbatar da yawan yan majalissar kafin suje nan, dakunan su da gidajensu basu kai darajar majalissar ba. Amma duk suka mance da haka saboda son zuciya.

Alhali ga kasa ana fama da matsaloli na rashin aikin yi, rashin tsaro, da sauran matsalolin yau da kullum.

A bisa wannan dalilin nake kira ga talakkawan najeriya su tashi tsaye su nemi abin da zai fishhsesu wajan biyan bukatar rayuwa, wallahi wadannan shugabannin namu basu da niyya da tunanin gyaran kasar nan. Kullum bukatunsu, su ne masu mahimmanci a wajan su. TALAKKA IDAN KUNNENKA YAJI TO JIKINKA ZAI TSIRA, IDAN KUMA KA ZAUNA KANA TUNANIN ZAKA SAMU INGANTACCIYAR RAYUWA A KARKASHIN WADANNAN SHUGABANNIN TO INA GANIN ZAI ZAMA JIRAN GANIN KAHON JAKKI NE.

Musa Ibrahim Daura
22-12-2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post