Suratul Hujurat ta koya Mana ladabi da girmama Matsayi na Darajan Manzon Allah (2)


-Sheikh Adamu Tsoho Jos.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Tare da Wakilinsu -Idishia Jos.
Allah (T) yana cewa; Ya ku wanda kuka yi imani Kada ku daga muryan ku sama da muryan Annabi (S), ko bama a gaban Annabi ba mutum yake ya zamo cewa kana daga murya kana magana da karfi to wannan baya daga cikin kyawawan dabi'u. Mutum ya zamo yana magana a daki ko a shago kowa yana jinka ko kana magana kai da mutum masu wucewa ma sai sun jika ana so idan mutum yana magana yayi magana cikin ladabi, ballantana kuma ace kana gaban ma'aikin Allah shugaban halitta to wannan wajibine ka kiyaye ladabi da maganan ka domin shi Manzon Allah (S) ba mutum bane kamar kowa.

A can aya na farko ance in yana tafiya kada ka wuce gaba shi in yana tafiya ko wajen wani aiki. A cikin Suratul Lukman Allah yana cewa; Ku kame muryan ku wato kuyi magana a hankali cikin nutsuwa domin mafi munin sauti shine sautin Jaki, nan ba wai magana akan kayi magana kamar bakkada lafiya bane a'a amma ba kuma ana so kayi kamar yadda Jaki yake kuka yake ihu ba haka ake son kayi magana ba. Ta yaya ya zamo cewa idan kana majalisin manya kana daga muryan ka kaga za'a ganka wani iri, to Rasulul A'azam Muhammad (S) shine shugaban Annabawa kuma shine mafi daukaka da daraja a halitta gaba daya dan haka dukkan wani ladabi da girmamawa da ainihin kankan da kai ya zamo wajibi akan mumini.
A cikin ruwaya dangane da wannan ayoyi guda Biyu da muka karanta yazo a cikin Sababun Nuzur, Allah (T) yana cewa; Ance wannan aya ta sauka ne akan tawaga na Banin-Tamim wanda suka zo wurin Manzon Allah (S), Sun kasance idan sun zo wurin Manzon Allah sai su tsaya a kofar gidan Manzon Allah (S) sai suce Ya Muhammad ! Da karfin gaske, kaga wannan ba ladabi ba girmanawa wannan rashin hankali ne da wauta. Musulunci ya koyar da mu bama Manzon Allah ba in kana tare da mahaifin ka kuna tafiya tare kada ka wuce gaban mahaifinka kada kuyi kafada-kafada dashi, kada ya zauna a kujera kai ma ka zauna sai dai in shi ya baka izini, kada in ana magana ka rigashi ko kasa bakin ka koko muryan ka yayi sama da muryan mahaifinka.

Imam Hassan in suna tare da Imam Hussain ba ya wucewa gaban Imam Hassan, baya magana in Imam Hassan yana nan sai dai in ya bashi izini, to wannan shine ake so mumini ya koya balle tana in kana gaban ma'aikin Allah Muhammad (S). To su wannan Banin-Tamim In sun zo wajen Manzon Allah sai suna kwalla mai kira da karfi, kuma su kirashi da sunan sa kai tsaye suce ka fito garemu mun zo. Kuma idan Manzon Allah (S) ya fito sai su wuce gaba gareshi suna tafiya wasu kuma suyi kafada da kafada suna tafiya wasu kuma sai su daga sautin su sama ga Manzon Allah (S). Sai suna ta fadin Ya Muhammad me zaka ce Dangane ga Abu kaza, Ya Muhammad me zaka ce dangane da Abu kaza ba ladabi BA girmama wa kamar suna magana da sa'ansu.

Shine Allah ya saukar da wannan aya din "Yaku wadanda kukayi imani indai imanin ku na gaskiya ne da Allah da Manzo to kada ku wuce gaban Allah da Manzo a magana ne ko a aiki." Kada kuyi magana sai in ya Baku izini in kuna tare a majalisin Manzon Allah (S) kada ku tashi sai ya baku izini, kuma kada ku daga muryanku kamar yadda aya ta ainihin bayani. Hadisi daga Ibn Abbas yake cewa; wannan aya ta sauka ne akan Sabit Bin Kais ya kasance wato baya ji sosai, Kasan wanda baya ji sosai in zai yi magana yanayi da karfi ne, ya kasance yana da murya mai karfi ya kasance idan yana magana yakan daga muryansa, wani lokaci ma yakan cutar da Manzon Allah (S) da muryansa. Sai Allah (T) ya saukar da wannan aya din.

To ance lokacin da aka saukar da wannan aya sai shi Sabit Bin Kais yaji wannan kuna yadda anas ya rawaito da yaki wannan aya sai ya koma gida yana ta kuka bataya fitowa Manzon Allah (S) baya ganin shi dai Annabi yayi tambaya ina Sabit yake sai aka ce ai yana gida sai aka kirashi sai Manzon Allah yake cewa ya bana ganin ka kwana Biyu. Sai Sabit yace Ya Rasulallah hakika an saukar da wannan aya kuma ni ina da murya mai karfi sai ina tsoron kada ya zamo na bata aiki na. Sai Manzon Allah (S) yake cewa ai kai ba da kai ne wannan aya take nufi ba, sai Manzon Allah ya mai bushara da kai zaka rayu cikin alkhairi kuma zaka mutu cikin alkhairi kai kana daga cikin 'yan aljanna wannan aya ba da kai take nufi ba.

Wannan wani bangare ne na karatun Tafsirin Alkur'ani Mai Girma da Sheikh Adamu Tsoho Jos ya gabatar jiya da dare a Zaman karatu na rana ta Biyu a muhallin Hussainiyatu Zakzaky (H) dake Unguwan Rogo Jos.
# FreeZakzaky .

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post