ZAMA DA MUTANE ASHARARAI DA KUMA MUTANEN KIRKI,
Daga Muhammad bn Kai's, daga Abu Jafar Muhammad bakir (a.s), daga kakansa(a.s) yace; Amirul muminin (a.s) yace;
"" zama da ashararai yana haifar da mummunan zato ga mutanen kirki.haka nan zama da mutanen kirki. Haka nan zama da mutanen kirki yana yana sauya asharari (yazama mutumin)kirki. Kuma zaman fajirai tare da mutane Na gari. Yana sa fajiran su zamo mutane Na gari.
"" Wanda al'amarinsa yashige maku duhu Baku San (gwargwadon rikonsa) ga addini ba, toku kuyi dubi zuwa ga abokan mu'amalarsa. Idan ma'abota addinin Allah ne, to shima akan addinin Allah yake, idan kuma ba akan addinin Allah sukeba, to shima ba akan addinin Allah yakeba, domin Manzon Allah (a.s) yakasance yana cewa; "" Wanda yayi imani da Allah da ranar Lahira kar yayi yan uwantaka da kafiri, kar kuma yayi aboki da fajiri. Wanda yayi yan uwantaka da kafiri, ko take mu'amala da fajiri, to za akalleshi amatsayin kafiri, fajiri"".
Naku; Mahadi Tukur Almizan
# FREE_ZAKZAKY .
Tags:
Makaranta