-Inji Shahid Kasim Umar Sakkwato.
Malam Kasim Umar wakilin yan uwa na Sakkwato ya yi wannan jawabin ne a wajen ta'alim wanda aka saba yi duk ranar alhamis.
A cikin jawabin Malam Kasim ya nuna cewa Shi'a ba wai shi ne ka sa bakaken kaya ba, a lokacin Ashura, amma idan aka yi mu'amala da kai sai a same ka babu kyakkyawan dabi'u.
Haka kuma Malam ya kara da cewa yafi kyau a gurin dan uwa ana ganin sa halakakke idan anyi mu'amala da shi sai a ganshi mutumin kirki .
Bayan nan kuma Malam ya yi kira ga yan uwa da su zama masu yin kira da ayukkan kirki fiye da kira da halshe. kamar yadda Imam Ja'afar (as) ya fada.
Haka kuma ya yi kira ga yan uwa su zama masu sallar dare ,
Inda ya bayyana cewa sallar dare tana karkare zunubi tana sanya kwarjinin fuska tana
sanya farin cikin rayuwa kuma dabi'a ce ta bayin Allah.
A cikin jawabin sa ya karanto wani Hadisi daga Jabir daga Imam Ja'afar (as) da yake cewa.
Ya kai Jabir ashe zai ishi mutum ya ce shi dan shi'ar mune ba tare da tsoron Allah ba, a'a wallahi ya kai Jabir ba kowa ne dan shi'ar mu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya yi da'a gare shi haka kuma shi'ar mu ba su kasance ana sanin su ba sai da tawadu'i, (kankan tar da kai), da kushu'i wajen sallah, da rikon amana, da yawan ambaton Allah, da.yawan azumi da sallah, da da'ar uwaye, da gaskiyar zance, da karatun Kur'ani, da kame bakunan su ga mutane sai da alheri, kuma sun kasance amintattu a cikin mutane. Don haka Kuji tsoron Allah ku yi aiki mai kyau.