Dole ne Gwamnatin Tarayya ta saki jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, wanda aka fi sani da Shi’a, Shaikh Ibraheem Zakzaky, da matarsa Zeenatuden Ibrahim, daga tsarewar da ake yi musu. A Samar Musu da wani masauki wanda dole ne a samar da shi cikin kwanaki 45, kamar Yadda wata babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da umarnin a ranar Juma’a 2,12, 2016
Sheikh Zakzaky da Mai dakinsa Malama Zeenatudeen Ibrahim da Sojoji suka kama a ranar 14, ga Disamba, 2015, suna hannun Mahukuntan Najeriya tun daga 15 ga Disamba, 2015 har Yanzu duk da Umurnin kotu da ta bada Umurni a sakesu.
Mai shari’a Gabriel Kolawole, yayin da yake yanke hukuncin hadin gwiwa a cikin kararrakin kare hakkin Mutanen guda biyu da Suka gabatar na Neman Yancin Su, ya ba da umarnin cewa ya kamata gwamnati ta samar da wuraren zama masu dacewa ga Mutanen biyu, da kuma mabiyan da suka kasance tare da su kafin a kama su.
Alkalin ya ba da umarnin cewa dole ne a samar da masaukin a Zariya, Jihar Kaduna, ko wani sashe na jihar ko kuma a wani bangare na Arewacin Najeriya a cikin kwanaki 45.
Alkalin ya bayar da Umurnin bayarda N25m, ga kowane daga cikin Mutanen Biyu, wanda yawansu ya kai N50m, ga Jagora Sheikh Zakzaky da matarsa, saboda take hakkinsu ta hanyar tsare su ba bisa ka'ida ba tun daga 14 ga Disamba, 2015 har Zuwa Ranar da yake yanke hukuncin.