--Idishia Jos.
Kotun ta bukaci a a saki Sheikh Zakzaky a tsawon kwanaki 45 ba tare da wani sharadi ba, kuma a biya shi Naira Milliyan 50 a matsayin kudin fansa.
A ranar 2 ga watan 12 sekarar 2016 Babban Kotu kasa dake Abuja ta umarci Gwamnatin Tarayya da a gaggauta sakin Jagoran Harka Musulunci Sheikh Zakzaky. A ranar 12/12/2015 gamayya jami'an tsaro na Nigeriya suka dira akan Almajiran Sheikh Zakzaky a Hussainiyyya Bakiyatullah wajen da 'yan uwa suke tarukan su.
Hoton Hussainiyyah Bakiyatullah Zariya kafin Gwamnatin Buhari ta rusa a 2015 |
Alkalin kotun Kolawale Gabriel ya ce tsarewar da hukumomi ke cigaba da yi wa Sheikh Zakzaky tun watan Disamban bara haramtacciya ce kuma ba ta da hujja a karkashin dokokin kasar.
Bayan Sojojin sun dira akan mutane a Hussainiyya daga nan suka wuce gidan Sheikh Zakzaky dake Anguwan Gyellesu inda su kai ta ruwan harsashi baji ba gani har ta kai ga sun kashe sama da mutane 1000+, tare da jikkata daruruwan mabiya Malam din. Sun kashe 'ya'yan Malam Zakzaky guda 3 Aliyu, Hammad, Da Humaid. Suka harbi Matar Malam Zakzaky har ta kai ga bata iya motsawa, shima basu bar shi ba suna ta harbinshi har sai da suka ga ya fadi a kasa jinin sa na tsiyayewa.
A lokacin da sheikh Zakzaky aka gano guragutsen harsasai a cikin kwakwalwansa. |
Sun tafi da Sheikh Zakzaky tare da matarsa bayan sun harbe su, sannan suka dibe gawawwakin da suka harba inda suka musu ramin bai daya aka binne su, ba tare da sun mikawa 'yan'uwan su ba. Wannan magana ta tabbata a lokacin da aka kafa Kwamitin binciken abinda ya faru na kisan kiyashin Zariya daga cikin wakilin Gwamnati yayi ikirarin cewa sun binne mutanen Sheikh Zakzaky a ramin bai daya.
Biyo bayan umarnin da Kotun Koli na kasa tayi fadar shugaban kasa tayi shiru da wannan umarni na babban kotu. Suka cigaba da tsare Sheikh Zakzaky har tsawon shekaru kusan 2 sannan kuma Gwamnatin Jihar Kaduma ta cigaba da tuhumarsa da kisan wani soja lokacin sojojin suka dira akan 'yan'uwa almajiran Sheikh Zakzaky a garin Zariya a shekarar 2015.
Jami'an tsaron sojoji a lokacin da suka zagaye 'yan'uwa a Hussainiyyah Bakiyatullah Zariya |
A wani jawabi na bidiyo da aka wallafa a shafin gwamnati na Twitter , wanda ya yi da jaridar Guardian, Mataimakin shugaban Kasa Osinbajo ya ce shi mutum ne da ke tsayawa tsayin daka wajen ganin an mutunta umarnin kotu.
Ya nuna cewa dalilin da ya sa gwamnati ba za ta saki shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta 'yan Shi'a Ibrahim El-Zakzaky ba, shi ne saboda ta daukaka kara kan hukuncin kotun da ya ce a sake shi.
Ranar Farko da sheikh Zakzaky ya bayya na a gaban 'Yan Jaridu a garin Abuja. |
Baya ga haka rundunan Jami'an tsaro na farin kaya DSS sun cigaba da rike Sheikh Zakzaky a garin Kaduna inda ake ta zuwa Kotu domin sauraren shari'ar da Gwamnati Kaduna ta shigar. Sheikh Zakzaky yana fama da tabarbarewan rashin lafiya hakan yasa wata babban a Kaduna ta yanke hukunci da cewa dole a bar wanda ake tuhuma yaje ya nemo lafiyansa a kasar India kafin a cigaba da sauraren shari'ar.
Har yanzu jami'an tsaro na DSS suna cigaba da rike Sheikh Zakzaky a Kaduna. |
A ranar Litinin 5/8/2019, wata babbar Kotun jihar Kaduna mai suna lamba 4 ( Court IV), Ibrahim Taiwo road karkashin mai shari'a Darius Khobo ta yanke hukunci kan barin a fita da Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky zuwa Kasar Indiya domin neman magani.
Kotu ta amince a fita da Malamin zuwa Kasar India domin neman magani bisa sharadda kamar aka:
- Zai kasance karkashin kulawar jami'an tsaron 'yan Sanda na DSS.
- Idan ya samu lafiya ya dawo, za a dawo Kotu domin ci gaba da wannan Shari'a.
- Idan ya samu lafiya ya dawo, za a dawo Kotu domin ci gaba da wannan Shari'a.
Babbar kotun Jihar Kaduna tayi Umarni da Sheikh Zakzaky yaje naman magani India. |
Bayan zuwan Sheikh Zakzaky Kasar India, Sheikh Zakzaky ya dawo ba tare da an duba lafiyansa ba saboda hadin bakin da aka samu tsakanin jami'an tsaron Nigeriya dana Kasar India domin su salwantar da rayuwansa. Wanda kuma Sheikh Zakzaky yayi jawabi a Bidiyo yake bayyana makircin nasu a sarari, kuma ita Gwamnatin bata musamta abinda ake zarginta da shi ba.
Zuwan Sheikh Zakzaky kasar India Domin kula da lafiyansa. |
Hakanan, gamayyar jami'an tsaro a lokuta dabam-dabam sun kashe daruruwan mabiya Shehin Malamin a kuma garuruwa dabam-dabam inda suka rika bude wuta kan 'yan 'uwa almajiran Malam Ibraheem Zakzaky a mafiya yawan lokutan da suke fitowa muzaharorin lumana domin neman hakkinsu na a saki Malaminsu da mai dakinsa da sauran daruruwan 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky da ake ci gaba da tsare su a Kurkuru.
Jami'an tsaro kusan kullum sai sun dira akan mabiya sheikh Zakzaky a wajen zanga-zangar lumana a garin Abuja. |
#FreeZakzaky