*SHARI'AR 'YAN'UWA 60 DA SUKA SHAFE WATANNI BIYAR A SARS ABUJA*


Tare da Shehu Al-ja'afaree Kaduna

Kamar yadda aka sani ranar 27/11/19 An daga shari'ar zuwa jiya 10/12/19 saboda yanke Hukuncin bada Beli ko a'a. Lauyan Gwamnati wato Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda Samuel Law ya soke maganar bada belin inda yace takardar Application din da Lauyan' Yan uwa wato Bala I Dakum ESQ ya kawo bai cika qa'ida ba saboda kamata yayi kowa ayi masa tasa daban har application guda 60 tare da counter affidavit.

Alkali bai wani 'bata lokaci ba ya yarda da wannan zancen inda har ya qara da cewa tunda garuruwan su daban kowa sai an fadi dalilin da yasa a keso a amshi belin shi tare da cikakken adireshin inda ya fito.

Lauyan yan'uwa yace wannan ba dalili bane saboda koda garuruwan su daban ai dukkan su a Abuja aka kama su don haka idan Har Kotu taso zata iya bada belin su domin beli ganin dama ne na Kotu.

A karshe dai Alkali yace bazai amshi wannan ba dole sai ya sake wani. Lauyan 'Yan'uwa Ya yarda zai sake. Alkali ya tambaye shi zuwa yaushe zai sake har ya kawo? 

Yace zuwa yau zai iya rubutawa har ya kawo, Alkali yace idan ya rubuta kuma ya kawo yau yaushe yake ganin 'Yan sanda zasu gama nazari har su bada amsa? Yace zuwa sati daya daga nan sai a dawo a duba.

Alkali yace ai sati mai zuwa kuma akwai hutun Kirsimeti dana sabuwar shekara.
Lauyan 'Yan uwa yace ko cikin hutun ai za'a iya zuwa a zauna. Lauyan Gwamnati ya mike yace bazai yuwu ba saboda wannan shari'ar a hana Kotu hutun da Gwamnatin ta bata.
Karshe dai an dage Shari'ar zuwa 05/02/2020 don cigaba da duba yuwuwar bada belin su ko a'a.

Maza su 54 an tura su Gidan Yarin Kuje, Mata kuma su 6 an tura su Gidan Yarin Suleja.
Sannan Kotu ta zartar da cewa a gidan Yarin Kuje za'a riqa shari'ar kamar yadda Lauyan Gwamnati ya nema. Wannan shari'ar dai kala biyu akeyi.

Mu Mun kai su Kara Federal High court Abuja. karar ne ma yasa suka kai 'Yan'uwan Kotu don basuyi niyya ba. wato State High court Apo Abuja. Ku samu cikin addu'a' Yan'uwa.

Zuwa yanzu' Yan uwa 76 ne a gidan Yarin Kuje, yayin da kuma 6 ke Suleja.
Ku riqa ziyartar su 'Yan'uwa don rage musu radadin kadaici.

#AllahSaveZakzaky(H)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post