SHAIKH ZAKZAKY BAWAN ALLAH!



SAYYID BAQIR ZAMILI, yana cewa: Malam Zakzaky(h) wata baiwa ce da mu'ujuza Allah yayi a Africa Wanda ke gwada A'imma (as) kiran da su kai tun farko ya kai karshen duniya. kiran Imam Husain wannan bawan Allah gwarzo ya amsa amma abin bakin ciki an taru duniya an dirar masa irin yadda aka yiwa Imam Husain, Sayyid Baqir yace badan siyasar duniya ba, da naje na bada Jinina an kasheni saboda wannan Malamin, saboda kamar na amsa wa Imam Husain ne.

Shi kuwa Sheikh Ahmad Nahadily Al- bagdadi cewa yayi: yakar Malam Zakzaky(h) ana so ne a ruguza Shi'a, yace da lokacin da Imam Husain yake karbala akwai bakar fata irin Malam Zakzaky lalle ba zai yiwu a kashe Imam Husain ba, don bakar fata suna da Imani da goyon baya na rai da rai, tabbas Allah ya bashi jajurtattun mutane, yace Malam Zakzaky ba iya na Africa bane, har a nan yana da mabiya.

Sheikh Najjar mai koyar da tarbiyya da gyaran ruhi dake Karbala cewa yayi, Ku sani duk inda ka tafi a duniya hasken Malam Zakzaky ya Riga ya daga muna ganin in Allah ya yarda sai mun taka Nigeria anyi wannan gwagwarmayar da mu kullum muna yi masa addu'a, lokacin da naji an harbe shi sai da naji kamar Imam Hujja(AF) zai bayyana.

Sheikh Murtadha Annajafy da akai hira dashi a wata tasha ta TV aka tambaye shi me yafi birge ka a tafiyar Shi'a sai yace babu abinda yafi burgeni kamar Malam Zakzaky, yace shine hasken da Allah ya tayar don ya gwada wa Shi'ar da suke nan yankin in basu iya taimakon addini ba ga wani can zai aiwatar, ya kara da cewa Malam Zakzaky Malami ne da ya wuce girman Marja'i wane marja'i ma, shifa wannan yana shiryatar da al'umma ne fa a Nigeria can ne ake shia tsantsagwaranta, karshe yace duk Wanda yake shia kaf idan yai ibada sai Allah ya kai wa Malam Zakzaky wannan ladar.

Sheikh Jamaludden cewa yayi yazo a cikin Hadisi daga cikin mataimaka Imam Mahdi akwai Ibrahimul Magribi to da naga Malam Zakzaky sai naji ina ma naje Nigeria na kai ziyara mai masa albishr da wannan hadisin, na godewa Allah da na hada zamani da lokacin da Ibrahimul Magribi yake. ruguza Malam Zakzaky ruguza Shi'ar duniya ne hatta IRAN sai ta samu gibi, ba'a taba samu ba wani yayi kira a kankanin lokaci a samu mabiya miliyan goma a tarihi, amma naji a hirar Saudiyya suna bayanin cewa Shi'a a Nigeria sun kai Miliyon 27 to kusan yawan Iraq ma miliyan 30 ne.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post