Sanin Ilimin AlQur'ani Sai Gidan da ba'acewa Babu..!!


'Ya'yan Manzon Allah (S A W.W) sun fi dukkan wasu 'ya'ya sanin haqiqanin ma'anar ayoyin Alqur'ani da kuma tawilinsu.

Shafin Ma'asumah Shafi Ne Domin Kai da Al'ummar ka.

Ya zo cikin hadisi in da aka ce Annabi (S) ya yi addu'a ga Ibn Abbas (R.A) kan Allah ya ba shi ilimin Alqur'ani, kuma Allah ya ba shin, amma duk da haka abubuwa sukan shige masa duhu wajen sanin haqiqanin ma'anar wasu ayoyin.
Za mu iya fahintar haka cikin sauqi in muka duba abinda ya faru wata rana a Madinah cikin masallacin Annabi (S.A.W.W).

Riwayar tana cewa;
Hassan ya kasance yana zaune cikin Masallacin Annabi (S), mutane sun taru kewaye da shi a gefensa, sai wani mutum ya zo ya sami wani gungun (mutane) wani na ba da labari game da Manzon Allah (S), mutane kuma na kewaye da shi.
Sai mutumin ya tambaye shi (me ba da labarin) kan cewa, ka ba nu labari game da (abinda ake cewa) SHAAHIDUN da kuma MASH-HUUD. Sai yace;
" Na'am, abinda ake nufi da SHAAHIDUN shine ranar juma'a, amma MASH-HUUD kuma ita ce ranar Arfa."

Sai ya wuce zuwa ga wani (na dabam) da ke bada labari cikin Masallacin, sai ya tambaye shi game da SHAAHIDUN da kuma MASH-HUUD kamar haka, sai yace;
" Amma SHAAHIDUN ita ce ranar juma'a, MASH-HUUD kuma ita ce ranar suka (Nahr) ."

Sai ya wuce zuwa ga na ukunsu ya tambaye shi game da SHAAHIDUN da kuma MASH-HUUD. Sai yace;
" SHAAHIDUN, Manzon Allah (S) kenan, MASH-HUUD kuma ranar Alqiyama ce. Ba ka ji Allah mai girma da daukaka na cewa;
" YAA KAI ANNABI! LALLE MUN AIKOKA NE MAI BA DA SHAIDA (Shaahidan) KUMA MAI BUSHARA DA KUMA GARGADI.."
(Ahzab, aya ta 45)

Kuma Allah (T) yace;
" WANNAN RANA CE DA MUTANE KE TARUWA GARE TA, KUMA RANA CE DA AKE HALARTARTA (Mash-Huud) ."

(Hud, aya ta 103)

To, sai ya yi tambaya game da mutum na farko, sai aka ce masa Ibn Abbas (R.A) ne, da ya tambaya game da na biyu sai aka ce masa Ibn Umar ne, da ya tambayi mutum na ukun nan sai aka ce masa shine Hassan Bn Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S).
Tare da Ado Isah Guda

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post