SALLAR JUMA'A

SALLAR JUMA'A

Tambaya Da Amsa Daidai Da Fatawar Syed Ali Khamenei

Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq Sokoto

T225- Menene fatawarka kan Sallahr Juma'a? Gashi kuma muna zamanin "Gaibar" Imam Mahdi ne, kana kuma idan mutum bai yarda da Adalcin Limamin juma'a ba, to shin wajibcin Halartar Sallar tana faɗuwa akansa ko kuma a'a?

Amsa- koda yake Sallar Juma'a a wannan lokaci namu wajibi ce Ƴar Zaɓi (wato tsakaninta da Sallahr Azahar) halarta ba wajibi bane, to amma saboda la'akari da Falalolin dake cikinta, to bai kamata ga Muminai su haramtawa kansu albarkar dake cikinta ba dan kawai saboda Shakkar adalcin Liman, ko kuma saboda irin waɗannan dalilai da basu da wani Muhimmanci.

T226- Menene ma'anar wajibi Ƴar Zaɓi a mas'alar Sallahr Juma'a?

Amsa- ma'anarsa shine mutum yanada zaɓi imma dai yayi Sallar Juma'a ko kuma Sallar Azahar.

T227- menene fatawarka kan Mutumin da ke barin Sallahr Juma'a saboda rashin ɗaukanta da Muhimmanci?

Amsa- barin Sallar Juma'a saboda rashin ɗaukanta da muhimmamchi abin zargi ne a Shari'a.

T228- idan mutum yana ganin Limamin Juma'a ba adali bane, ko kuma yana shakkan Adalcinsa, to shin ya halatta ya bishi don kiyaye Hadin Kan Musulmi? Kana shin yana halatta ga wanda baya Halartar Sallar juma'a da yayi ƙoƙarin hana sauran mutane halarta?

Amsa- baya inganta gareshi daya bi mutumin da baya ganinsa adali, ko kuma yake Shakkar Adalcinsa, kuma Sallar da yayi abayansa bata inganta ba, to amma babu laifi yayi hakan dan kiyaye Haɗin kan Musulmi, to amma a kowacce hali dai bai da damar da zai kwaɗaitar da wasu akan barin Halartan Sallar ko kuma ya ƙarfafa su kan hakan.

T229- to yayin da Mutum yake Shakkar ko kuma ma yake da Yaƙinin rashin adalcin Limamin Juma'a, kana ya riga yayi Sallolin Juma'a abayansa, to shin dole sai ya sake su?

Amsa- idan har Shakkar kan Adalcinsa ko kuma Yaƙinin rashin adalcin bayan Idar da Sallah ne, to Sallolin nasa sun inganta, kuma va wajibi bane ya sake su.

T230- Mutumin da bai samu damar Halartar Sallar Juma'a ba, shin zai iya yin Sallar Azahar da La'asar ɗinsa tun farkon shigar lokaci? Ko kuma wajibi ne ya jira sai an Idar da Sallar Juma'a kafin yayi su?

Amsa- ba wajibi ne jira sai an Idar da Sallahr Juma'a ba, ya halatta yayi Sallolinsa na Azahar da La'asar tun farkon lokaci.

Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Sokoto 08132933333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post