"Na ji yan kwanakin nan ana ta cewa mutane wai ana taya su murnar shiga sabuwar shekara (ta Turawa), abin bakin ciki har da Musulmi (a junansu), sai ka ga Musulmi ya hadu da dan uwansa Musulmi ya ce masa "Happy New Year!" Barka da shiga sabuwar shekara, har ana tattaunawa cewa wannan sabuwar shekarar ko me ta zo da shi!!
"To gaskiya mu dai ba shekararmu ba ce! Yauwa! Shekara a wajen Allah da Mala'ikunsa (ita ce shekarar Musulunci), to wannan shi ne farkon shekara. Kuma shi ne ya kamata a raba Alewa a taya juna murna!!"
Shaikh Zakzaky (H): Ranar Laraba 28- Zulhajji- 1428. A karatun Nahjul- Balagha, daidai minti na 46, a FIC Zariya.
A LURA!!
Zahirin magana anan, Jagora (H) yana magana game da taya juna murna a tsakanin Musulmi yasu- yasu ne, ba hani yake ga yi wa kiristoci murnar sabuwar shekarar ba.