Sai An Yanke Tsammani , Taimakon Allah ke Zuwa !!!


Haka Allah ya tsarawa kansa kuma ba a tambayar dalilim haka, domin shine masanin komai da hikima wajen tsara al'amransa (S.W.A).

@ MA'ASUMAH NIGERIAB NEWS UPDATED @ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

AMMA TSANANI SHINE ALAMUN ZUWANSA



Qur'ani ya kawo mana qissosin Annabawa da Manzanni (A.S)yadda suka yi gwagwarmayarsu cikin cutarwa, qaryatawa da kuma muzgunawa, amma babu wanda yayi nasara cikin sauqi kuma a qanqanin lokaci har sai bayan yanke tsammani da samun taimakon nasara daga Allah sannan tazo musu.

Duk wanda ya tsaya qyam ya dake kan tsarin Allah, to, zai cutu fiye da yadda wawaye ke tunani, amma masu hankali sun san haka hanyar take.

Za ka ji mutane na tambaya wai, YAUSHE NE TAIMAKON ALLAH ZAI ZO MUSU NE YAYIN TSANANIN AZABTARWAR DA SUKE CIKI ?Har ma ka ji dolaye na yi musu izgilanci kan haka.

Allah (T)na cewa;

" HAR A LOKACIN DA MANZANNI SUKA YANKE TSAMMANU (na samun nasara da taimakon Allah), KUMA SUKA YI ZATON CEWA AN QARYATA SU (ta hanyar rashin kawo musu agajin gaggawa), SAI TAIMAKONMU YA JE MUSU, SA'AN NAN MU TSERATAR DA WANDA MUKA SO, KUMA BA A MAYAR DA AZABAR MU DAGA MUTANE MASU LAIFI ".

  (Suratul-Yusuf:106)

Saboda haka haquri dai za a qara, taimakon Allah na nan kusa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

   08126385470

~ 10th Dec, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post