Sai Kun Qure Zaluncin Ku Sannan Ku dau QasQanci a Karshe !!!


KAMAR YADDA KUKE CUTAR DA BAYI HAKA ALLAH ZAI MUNANA QARSHE KU

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

Ba a hana azzalumi yin zaluncinsa sai dai a fada masa gaskiya ko zai shiryu. Amma dai abinda ba za ku taba kauce masa ba shine daukar qasqanci a qarshen rayuwarku.
Shi azzalumi ba ya tunanin cewa akwai qarshen wannan zalunci nasa, a kullum tsammani yake zai dore tare da dawwama a duniya ko kuma cikin damar da ya samu wacce yake amfani da ita wajen zaluncin nasa.
Abinda ba ni da kokonto kansa shine, azzalumai ba za su iya ganin bayan Sayyid (H)ba sai dai kawai su yi iya zaluncin da za su iya a kansa kafin daga baya su kunyata tun, daga nan duniya ka fin lahirar su ta zo.
Dalilin wannan fadin nawa ko kuma tabbacin da nake da shi shine, Sayyid Zakzaky(H)Mujaddadi ne wanda Allah (T) ya samar da shi a doron qasa don yi masa wannan aiki nasa na musamman.
Kaf littafan tarihi sun kasa kawo gurin da aka ambaci cewa azzalumai sun yi nasara kan wanda Allah ya tayar don isar masa da saqonsa.
Yaa ku azzalumai, ku zauna da shirin daukar qasqanci (ZILLAH)nan ba da jimawa ba insha Allah, domin alamu sun nuna cewa qarshen ku ya yi kusan daqushewa ta hanyar wannan kira da Sayyid Zakzaky (H)ke yi da ya ratsa dukkan sassa na duniya.
Sunan wannan abinda kuke yi na yanzu shine nade tabarmar kunha, domin kun rasa abinda za ku iya dogara da shi ku sake shi (H)tunda kun riga kun bar wannan dama taku.
Ku sake shi (QASQANCI)ne gare ku, haka ma cigaba da tsare shi qasqanci ne a idon duniya.
Daga wakilanmu na zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~ 5th Dem, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post