Nima Gargadi kawai Nake yi Muku !!!

HAR YANZU LOKACI BAI QURE MUKU BA

Addinin Allah gargadi ne, amma fa ga wanda yayi imani da Allah da Manzonsa (S.A.W.W)da kuma ranar lahira. Saboda hakane naga ya dace na qara yin gargadi ga dukkan wani azzalumi da kuma mai goyawa zalunci baya.

Akwai lokacin tuba ga duk fajiri azzalumi ko kuma mai aikata wani sabon Allah matuqar yana cikin hayyacinsa, kuma bai zo gargara ba.

Kada wani azzalumi ko mai sabon Allah yaga yana cigaba da rayuwa lafiya yayi tsammanin abinda yake yi daidai ne, ko kuma wata yarda ya samu a wajen Allah har yake yin abinda yaga dama ba tare da fargabar wani abu ba a fahintarsa.

Wani jinkiri ne da Allah ke yiwa mutum ko ya gyaru, ko kuma dai zuwa wani ajali ambatacce wanda ake sauraron zuwansa.

Mu dau darasi daga Fir'auna mana, da kuma na wannan zamani irin su;
Abacha,
Saddam Hussaini, da kuma
Musa 'Yar Aduwa. Dukkansu babu wanda yayi imani cewa Allah fa Allah ne.
Allah (T)na cewa;
‘’ KUMA DA YAWA DAGA ALQARYA NA JINKIRTA (yi musu azaba)ALHALI ITA AZZALUMA CE, SA'AN NA KAMA TA, KUMA ZUWA GARE NI MAKOMA TAKE.
KACE, ‘’ YAA KU MUTANE ! LALLE NI FA MAI GARGADI NE KAWAI ZUWA GARE KU, MAI BAYYANAWA.

TO, WADANDA SUKA YI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAWAWAN (ayyuka bayan munanan da suka aikata), SUNA DA GAFARA (a wajen Allah)DA KUMA ARZIQI NA KARAMCI.

KUMA WADANDA SUKA YI AIKI (na muni)CIKIN AYOYIN MU, SUNA MASU GAJIYARWA (ga muminai), WADANNAN 'YAN (wutar) JAHANNAMA CE ‘’.
(Suratul-Hajj, aya ta 48-51).
ALLAH YASA KU GANE.
Tare da Ado Isah Guda.
~ 3rd Dec, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post