...Namijin Maza Mai Kare Karfin Ikon Allah ..,!!!


Yazo cikin littafin Akhlaƙ A'immah shafi na 52, wata rana Abu Hanifah, Malamin Ahlul Sunnah ya gayawa Imam Ja'afar As-Sadiƙ (As) cewa,

"Yaronka, Musa Ibn Ja'far (As) yana sallah ta yadda mutane ke hucewa suna tsallaka Sallarsa.

Shin hakan bazai taɓi wani sashi na tawali'unsa ba?" Imam yace, "Zan kirashi, saika tambayeshi kai da shi" Bayan an sanar dashi wannan ƙorafin.

Sai yace, "Wanda nake wa Sallar nafi kusanci dashi gaba ga waɗannan mutanen.
Shine da kansa yace, "Munfi kusa da mutum fiye da lakkar jijiyarsa".

Tunda yaji haka fiskar Abu Hanifah ta cenja, sabida baida abinda zai iya cewa.
Imam Ja'far As-Sadiƙ (As) ya rungumi ɗansa yace, "Namijin maza, mai kare ƙarfin ikon Allah"
Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad√√√√√
Sakon Barka da Safiya
_____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post