Na Tausayawa Tukur Burtai da Rundunar sa !!!


'Zakzaky ka fito kafin na kirga Uku ko na rubza gidan a kanka!'

'Mun kashe Shi'a sauran Zakzaky! Ka fito Zakzaky yau za mu kashe ka!'

Wannan kadan kenan daga irin kalaman da Sojojin da Njeriya da kwamandansu suke dinga yi suna ihu da sowa a kofar gidan Sheikh Ibrahim Zakzaky bayan sun kashe dukkanin mabiyansa da suke kewayen gidan.

KARO DA SHI'A BABU DADI.
Wannan shi ne taken labarin na.Amma sai na fara da Karar farautarsa Azzaluman Duniya, wanda suke maida shi kamar Rakumi da alaka, sai abin da suke ce masa shi da Ogansa Dan Adamu mai Agwagwa.
Ba mamaki Makiya su yi dari su ce Uhmm ka ji Kuri ba Buratai ne ya Ci Ubanku ba har guduwa ku ka ke yi, Sojojinsa sun kashe ku sun kashe Matanku da Yayanku har sun yiwa Matanku Fyade kafin su kashesu. Shin ba kuna gani bane aka rushe Mahallinku na Husainiyya da gidan Shugabanku da Makabartar 'Yayan da Gwarazanku, shi kuna ina ne El Rufa'a ya rushe Kabarin Mahaifiyar Zakzaky? Sannan za ku zo ku ce mana wai fada d Shi'a babu dadi. Idan kun isa ku kwato Zakzakin naku mana ku daina damunmu da 'Dole a Saki Zakzaky' Ku huta muma mu huta.

Uhm Gaskiya Dan Izala abin da ka fada duk an yi mana. Amma Yaro bari Murna Karenka ya kama Zaki ba ka sani bane.
Ina Tausayawa Buratai saboda daga jin sunansa Musulmi ne shi, kuma harshen mu daya dashi sannan al'adunmu daya da shi. Sannan shi Mutum ne kamar ni kafin ya maida kansa Karen Yahudawa. Mu a addinimu an ce dukkan Mutum kodai dan uwanka ne a Addini ko kuma dan uwanka ne a Mutuntaka. Saboda haka na tausaya masa da ya sayar da Lahirarsa har da Duniyarsa ma bai sani ba, sai yanzu ya fara fahimta. Akan alkawarin Mulki da yan Kudaden da Wahabiyawa suke bashi ladan aikinsa, ya yi hannun riga da Rahamar ubangijinsa. Menene a wannan Duniyar da har zai rudi Mutum mai hankali ya sayar da Lahirarsa da ma jin dadin Duniyarsa akan wani abu da ba matabbaci ba?
Lokacin da Buratai ya zo Zariya da nufin shekar da jinanan Shi'a ya kama Zakzaky ya kashe shi kamar yadda suka yiwa Muhammad Yusuf, ya zo cike da Izza da karfi na Makamai da goyan bayan Gwamnatin Najeriya da Isara'ila da Amurka da Saudiya, yana jin cewa duk Najeriya ba wani wanda ya ke gabansa hatta Ogansa Dan mai Agwagwa.

Buratai da Yaransa sun dauka aikin da aka ba su ba zai dauke su Sa'o'i Uku ba, amma ina sai ga Wankin Hula ya kai su dare.
Farko Mu ba Yaki mu ka zo ba, amma Buratai ya yi shirin Yaki kamar zai Gwabza da Wata kasa mai karfin Soja. Duk da shirinsa sai ya kasa fitowa ya ce 'Yau Rundunar Sojojin Najeriya za su kauda yan Shi'a sannan kuma su kashe Shugabansu' Amma sai bai iya yin haka ba. Sai suka ce Wai an tare musu hanya. Wannan Shirin Shaidai ya kawata musu shi sosai don nan da nan Kafafan Yada Sharri irinsu BBC da VOA suka dinga Maimaita cewa Buratai ya tsallake rijiya da baya. Bayan karyar ta yadu a duniya sai kawai cikin dare suka fito da Mugun Nufinsu. Saboda su ta'addancin da suke son yi kafin dare ya yi. Ga wanda yake bibiyar lamarin zai gane cewa Buratai ya so ya yi Ta'addancinsa da rana ne amma sai ya ga sauran yan uwa za su kawo dauki, don kare Shugabansu, don haka ma Iyayengidansa suka zabi lokacin da Yan uwa ba su fara tururuwa zuwa Maulidi ba, lokacin da aka gama Tattaki kafin Maulidi ya zo. Da Buratai Jarumi ne da sai ya zabi lokacin Tattaki ko kuma Lokacin da mu ka zo Muzaharar Maulidi sai ya ayyana abin da ya zo ya yi akanmu. Amma Buratai ya ji tsoro don haka ya Shammace mu. Ba mamaki wani ya ce ai Yaki haka yake, dan Zanba ne, sai mu ce to ai mu ba Yaki muka fito ba, ba kuma Yaki muke da wasu ba. Kuma ba mu da makamaai, babu wani dalili da Mai Makamai zai yi mana kwanton Bauna,dan ba Matsoraci bane. Amma haka aka tsarawa Buratai.

Buratai da rundunarsa sun yi mana ruwan Wuta babu tausayi ba tare da bin Ka'idarsu Yaki ba. Sun yi amfani da Manyan Makaman Yaki irinsu Tankoki da Motoci masu Sulke da RPG(Rocket Propel Granade" sun yi amfani da Bomb da Shell da Gurnet da Bindigogin Snipers Rafle, da Mashingan Iri iri. Wasu makaman ana amfani da sune akan Tankokin Yaki da Motoci masu Sulke wasu don tarwatsa Ramin Karkashin Kasa. Amma haka suke shafe awowi sama 48 suna ruwan Wuta akan mu ba mu da komai sai dai idan ka ga Dutse a gabanka ka dauka ka yi Jifa da sunan Allah. Babu Jarumta ga duk rundunar Sojan da take dauka wannan lokaci ta kasa Murkushe marasa Makami. Ganin asirinsu ya toni sai suka dinga amfani da 'Shell' suna cinna Wuta a cikin Yan uwa. Sun Kone Mutane da yawa wasu Gawarwakinsu kona wasu kuma da ransu suka konesu.

Rundunar Buratai sun yi dukkan wani nau'in ta'addanci da ransu zai iya sauwala musu akamu. Sun ci zarafin Matanmu sun tarwatsa Gawarwakin yan uwa. Sun kashe Yara kanana. Wani abin Jarumta wasu Sojoji suka yi a Husainiyya sun je wani daki da aka rufe Yara kanana a cikin da suke ta Kuka saboda ruwan Wutar da ake a cikin Husainiyyar, suna balle Kofar sun harbesu gabadayansu, Wani Jarumin Soja bayan ya kashe Uban Wani Yaro, Yaron ya taho yana Baba! Baba sai kawai ya sa Bindiga ya harbeshi. Irin wannan Jurumtakar suka ka yi akan Yara Mata Matasa harbi a ka ko a Kirji ko a Kahon Zuciya.

A takaice dai sun yi kasa kala-kala sun kone Yara sun Kashe Iyayensu Mata bayan sun yi musu Fyade sun saka Wuka sun farka Matancinsu, wasu sun saka bindiga sun harbi gabansu. Suna Ihu suna kafin ku je Wuta. Duk wani Dabbancin ba irin wanda ba su yi mana ba. Abin da suka yi mana ya shige Dabbanci, saboda dabba hatta ta Dawa ba ta kashe Yar Uwarta dabba don kawai ta fi ta karfi ko don ta Isa ko don Wata Dabba ta umarceta. Dabbobin Dawa masu cin Nama suna kashe Dabbo yan uwansu idan suna jin yunwa kawai. Amma ba don isa ba. Amma Sojojin Najeriya sun yi mana haka, abin da Dabba ba za ta yiwa Dabba yar uwarta ba.

Idan ka tambayesu me ya sa Kuka kashe Yara a cikin Husainiyya sun tare muku hanya ne, ba za su iya ba ka amsa ba. Ko ka Tambayesu da wacce hujja ku ka kai hari gidan Sheikh Zakzaky har kuna cewa za ku kashe shi, kun kashe Shi'a Saura Zakzaky, Shin kuna kare Wahabiyanci ne ko kune baradan Izala ko Dakarun Kare Sahabbai duk da wasu a cikinku ba san su waye Sahabbai ba. Ko ka tambayi Buratai me ya sa ka ba da Umarni aka Kone gawarwaki bayan kun kashesu, me ya sa kuka kone wasu da ransu? Shin ba ka ce yan Shi'a sun karya doka bane shi ya sa ka ke kashesu? Wacce doka ce ta ce idan an karya dokar kan hanya hukuncinsa Kisan Kiyashine. Shi a dokar Soja ba haramin bane kashe wanda ba shi da Makami? ..... Za mu ci gaba.

Copy Daga Shafin Internet Froum


SAUKE APPLICATIONS DINMU A WAYAR KA YANZU DOMIN SAMUN AYYUKAN MU AKOWACE RANA. GA APPLICATIONS DINNAN 👇👇👇👇


Kasancewa Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post