@Ma'asumah Nigeria News Updates
@Shafi Domin Kai Da Al'ummar ka
_____________________________________
-An ruwaito mana daga Ibrahim Hashim ya karɓo daga Yahya Bin Abu Umran daga Yunus daga Jameel wanda yace naji Abu Abdallah (As) yace,
-Mutane sun kasu kashi uku; masana ilimi, masu neman ilimi da da Marasa amfani.
-Kuma mune masana ilimi (As), Ƴan Shi'armu masu neman ilimi, Sauran al'umma kuma marasa amfani ne.
-An ruwaito mana Mubammad Bin Isa daga Alhasan Bin Ali Bin Fazaal daga Al-Husaini Bin Usman daga Yahaya Bin Haib daga Babbansa Abu Jafar inda yace nida shi muna tare Hasanul Basary ya ruwauto yaji Manzon Allah (S) yace,
-Wanda ya ɓoye iliminsa to, a ranar Ƙiyama za'a tasheshi ɗaure da sarƙoƙin wuta.
-Sai yace, menene kuma ma'anar faɗar Allah a cikin Al-Qur'ani mai girma "Mai imani daga cikin mutanen Fir'auna (La) ya ɓoye imaninsa sabida kisa da akewa wanda ya ambaci Allah?.
-Sai Abu Jafar (As) ya ɗaga muryarsa yace, Zai iya zuwa duk yadda yake so yaje, amma na rantse da Allah bazai sami ilimi ba saidai anan.
-Bayan shiru daya biyo baya naɗan lokaci, Abu Jafar (As) yace, "Tare da iyalan gidan Manzon Allah (S).
-A wata ruwaya kuma Ahmad Bin Muhammad ya karɓo daga Al-Husain Bin Ali daga Abu Ishaq Abu Taibat daga Abu Maryam wanda yace,
-Abu Jafar (As) ya faɗawa Salmat Bin Ƙhalid da Al-Hakam Bin Utaibah: 'Koda zakuje gabas da yamma, kudu da arewa bazaku sami cikakken ilimi ba har sai daga abinda ya fito daga garemu (Iyalan gidan Manzon Allah).'
-Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad..........
-Don ƙarin bayani
Duba littafin Basaair Al-Darajat, Shafi Na 14.
____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
Tags:
Taskar ilimi