Dasunan allah mai tarwatsa azzalumai, da masu goyon bayansu,
Nayi niyyar yin wannan rubutun nawane abisa
wani tunani nawa, musamman akan musuluncin
Dan Nigeria.
Naba wannan rubutu nawa sunan musuluncin
Dan Nigeria shidai yayi sallah*
Dayawan musulmin qasata Nigeria sundauka
kawai musulunci shine kawai kayi sallah, kaci
tuwo ka kwanta kayi barci, katashi kaje kanemi
kudi, kawai haka Dan Nigeria ya dauki addinin
musulunci.
Natsaya nayi tunanin banga qasar da akadauki
sallah da mahimmanci kamar Nigeria ba, zakaga
da zarar ankira sallah zakagansu sun nufi
masallaci, da Wanda yasan yadda ake sallan da
Wanda bai Sani ba duk haka suke tururuwan
zuwa masallaci.
kisan kai
Musulmin Nigeria da yawansu basu sannan miyehukuncin kisan kaiba batare da wani dalili ba,
shidai kawai babu ruwansa, bilhasalima shi idan
anyi kisan kai dadi yakeji, indai bashi aka
kasheba to kisan kai ba wani abin damuwarsa
bane.
Banbancin fahimtar musulmin nigeria
Musulmin Nigeria sundauki banbancin fahimtaamatsayin kamar addinin kowa daban ne, Dan
darika yana ganin Dan izala ba musulmi bane,
haka Dan izala yana ganin Dan shia kafurine
kamar yadda suke fadi.
Shiyasama yanzun ana kashe 'yan shia anigeria
kusan dukkan malaman qasar nan sunyi shiru,
wasu sunacewa hakan daidaine harma suna
fadar zasu bayar da gudunmuwa wajan aiwatar
da kisan kai ga 'yan shia.
Wasu kuma malaman sun nuna qin amincewarsu
akan kisan da akeyi.
Babban matsalar musulmin Nigeria
Dayawan mutanen qasata kuma musulmi, akwaijahilai dayawa musamman matasa.
Shiyasama sai kaga mutum bai San komi amma
kaji yace wane yana zagin sahabbai, wane
kafurine wane mushuriki ne, amma da ka
tambaye dalili sai yakasa Baka amsa, idan ka
kaishi bango sai yace ai akaset din sheikh wane
yaji, Dana sheikh wane.
To shiyasa malamai suke qara lalata komi a
Nigeria, sukansu shuwagabannin qasar akwai
qarancin ilimin addini akwakwalensu, shiyasa
basu dauki kisan mutum abakin komi ba, muddin
kujerar mulkinsu zata cigaba, haba kwana
nawane zakaga bar kujerar mulkin??????
Kuma kai dakake kisan kana tunanin kai bazaka
mutu bane???
Idan ko har kaima zaka iya mutuwa, to kasani
zaka hadu da mummunan sakamako.
Haka kaima mai goyon bayan ta'addancin zaku
tashi tuta daya damai kisan kan.
*Allah yayi mana jagora yakuma dawo mana da
Sayyed zakzaky cikinmu