Mlm Zeena A Jawabinta Ga Harisawa tana Cewa:-


Yi Shiyarin Domin Amfanar Wasu...
@Ma'asumah Nigeria News updates
@Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

MA'ANAR NASARA GA MUMINI

Nasara shine ka koma ga Allah kana ga Allah kana yardajje a wajensa, ba wai addinin Allah ya tabbata kana gani ba. Don yana Iya yiwuwa lokacin da ake gwagwarmayar kana da Iklasi, kana yi tsakani da Allah, kuma da a lokacin ka samu Shahada Aljannarka tsaf! To, amma idan addini ya tabbata (kana raye) tunda ana cigaba da jaraba mu ne, in ka ci jarabawar farko ba yana nufin lazim za ka ci na gaba bane. Kamar dai a makaranta ne, in ka ci wannan jarabawar ba Sai Kuma ka saki jiki kace tunda na ci shikenan zan ta ci ba. A'a, za ka yi ta kokari ne don gaba.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

 To yana Iya yiwuwa bayan addinin ya tabbata kana raye ka dawo Kuma ba don Allah kake yi ba. Yanzu Kuma kana son mukami ko abin Duniya ne. Kila kace ga wasu nan suna jin dadi, kai ma kace yanzu kana son jin dadin nan. Sai ka mance ma hadafin zuwa Duniyar. Don haka hakikanin nasara kawai shine ka koma ga Allah kana yardajje, ka cimma abin da ya kawo ka Duniya dominsa."

— Malama Zeenah Ibrahim, a jawabinta ga Harisawa ranar 28/9/2014.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post