MENENE SO
Ma'asumah Nigeria News UpdateIshaq Sokoto
To shi so wani tsarkakakken abu ne Wanda ba'a ganinsa da idanu sai dai alamomi su tabbatar da samuwarsa
Sannan shine gundarin saƙon Addinai
Da kiran Manzani
Idan kaso kace shine rayuwa ko kuma sirrin dake sa rayuwa ta cigaba
Duk inda kaga wata matsala ta faru to so baizo gurin bane
Wannan yasa manazarta ke ƙoƙarin ɗora rayuwarmu mutane akansa
Saidai kasancewar sa me tsarki sai yazama baya karɓar datti
Babban abinda yake hanamu ganin tasiri da natija ta so shine datti da muke baibayeshi dashi
Annabi Yusuf (As) ya gayawa zulaikha cewa:(kidena kiran kina so na domin shi so me tsarki ne abinda kike nufi kuma datti ne Wanda so baya karbarsa)
Amma yayinda Zulaikha ta riski so na gaskiya saigashi har aure ya hadata da Annabi Yusuf
To irin dattin da muke gogawa so sun haɗa da
Yaudara
Qarya
So saboda wani dalili
Kamar kyau ko dukiya ko muƙami
Domin asalin abinda zuciya take yiwa so shine (jamalul mutlaq)
Sannan duk abinda kaga zuciya ta dimauce da sonsa to ta hango tajallin wannan jamalar ne a cikinsa
Saboda haka da zamu dinga kallon Allah a cikin komai da kowa sannan musami narkewa da zagwanyewa a cikin Allah da mun zauna lafiya.
Allah kabar mu da Soyayyar Manzo Da Ahlinsa
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Sokoto
Tags:
Kalaman Soyayya
Allah ta'ala ka gafartawa mawallafin rubutun nan, ka sada shi da ceton fiyyayen halitta (saww).
ReplyDeleteHar yau muna kewar rashinka a tare damu ya shaheeed.