-Wata rana wani mutum yana magana da abokinsa sai Manzon Allah (S) yaji abinda ya faɗa a karshen maganarsa.
-Ga abinda ya faɗa ɗin kamar haka: "Bana son mutuwa" sai Manzon Allah (S) yace masa kana da dukiya, yace "Eh" sai Manzon ya ƙara tambayarsa, "Ka taɓa yin hadaya ko sadaƙa? Yace, "A'ah. Manzon Allah (s) yace, "Wannan shine dalilinka na ƙin son mutuwa.
-Imam Sadiq (As) yace, "Wani mutum yaje wajen Abu Dharr Al-Gifari ya tambayeshi, "Wai menene yasa bamu son mutuwa? Sai yace, "Sabida ka shirya jin daɗin duniya baka hange n makomarka ta lahira", kuma mutane basu son su matsa daga wajen da suka shirya lallata.
-Aka Tambayi Abu Dharr, me kake tunani dangane da komawarmu ga Allah, maɗaukakin sarki? Yace, ga masu kyautatawa zai zama kamar mutum ne da baya nan ya dawo ga mutanensa.
-Ga mugaye, kuma zai zama kamar bawane daya gudu zai dawo ga uban gidansa cikin firgici da tsoro. An tambayeshi, "Menene matsayinmu a wurin Allah?
-Yace, "Kayiwa kanka hisabi da littafin Allah, domin ya faɗa cikin suratul Infiɗar Ayata 13-14, "Haƙiƙa, salihan bayi zasu zauna a tsakiyar ni'ima, kuma lallai mugaye a gidan wuta suke".
-Mutumin yace, "To, ina rahamar Allah? Sa yace, "Haƙiƙa rahamar Allah tana kusa ga masu aikin alkairi." Suratul A'araf Ayata 56.
Allah ka azurta mu da samun rahamarka don habibinka Muhammad (S).
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈