MAZA SUN SHA GUDU A GARIN JIBIYA



Ranar lahadi 29/12/2019 ana kashe janaretan masallacin Attakawa dake unguwar waliyyi bayan sallar isha'i sai wasu mutane fiye da mutum 10 kowane da doguwar rigar sanyi su nade kansu da rawani kuma dauke da Bindiga suka zo kusa da masallacin inda mutane ke zazzaune suka zagaye wasu mutane 2 dake gefe zaune kan benci sannan suka cacukumi guda suna tunanin shi ne saradaunan Jibiya Alh. Tasi'u Waliyyi. Sai Ibrahim Buraima yace masu bani bane,  daga nan suka anshe dukkan kudin shi da wayarsa sannan suka jashi tare da wani Mutum mai jinyar kafar shi suka aje su bayan Janaretan gidan sardaunan, daga nan suka shaki mai gadin gidan suka shiga dashi cikin gidan sardauna inda suka kwace kayan adon mata sannan suka fito da uwargidan sardauna da kuma goyonta suka kuma hada da sakataren shi. Akan hanyarsu ta gudu suka yi wani irin harbin mai kan uwa da wabi inda ya samu wani matashi  tela dan shekara 21 ga kugu kuma harbin ya yi sanadiyar mutuwarsa. 
Acikin 'yan mintoci kadan labari ya bazu cikin gari, jama'a suka fara gudu zuwa inda zasu boye maimakon kai gudunmuwa inda abun ya faru. Dukkan gari sai rufe shaguna ake ta yi wasu ma an kasa rufewa don tsoro an  ruga. Ya Salam ! A gaskiya abin takaici ne abin kunya kuma abin tsoron yadda rayuwarmu zata kasance nan gaba. 

Na san mai karanta wannan labari ko sauraro zai yi mamaki matuka ace Barayin da basu kai 15 ba su zo tsakiyar garin Jibiya da kafafuwansu su yi abinda suka ga dama kuma su gudu ba'a kama ko 1 ba. Ina mazan suke ? Ina jami'an tsaro ? Ina 'yan banga ? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. 

Tabbas ga bakon da zai tafo daga katsina in yaga yadda aka kafa shingayen jami'an tsaro fiye da goma sha, kuma kusan ko ina direba sai ya tsaya yayi rijista irin tasu ta direbobin Najeriya zai yi mamkin jin abinda ya faru a tsakiyar garin Jibiya kuma bayan sallar  isha'i.

Limamin masallacin dana yi sallar Asuba ya yi mana nasiha akan cewa mutane su rage tsoro kuma su kara gyara imaninsu ta hanyar dogaro da Allah da kuma barin biyar bokaye da malaman tsibbu masu bada layu da karhu a matsayin maganin bindiga, wuka da makami iri daban-daban.
Malam Ya kuma tunatar da mu hadisin manzan Allah s.a.w. Dake cewa duk wanda ya rasa ransa wajen kare mutuncin iyalinsa, dukiyarsa ko al'ummarsa to ya yi shahada, shin tsoron me muke ji ko hadisin ke bamu yi imani da shi ba.

Daga karshe ya ummurce mu da mu ba azkar muhimmanci, in zamu fito daga gida mu yi addu'a, wannan na daga cikinsu Tawakkaltu alallah, Lahaula wala kuwata illa billah., mu rika karanta Ayatul kursiyyu, suratul ikhlas, falaki da nas duk bayan sallar farillah. In mun tunkari azzalumi mu karanta Allahumma aj'aluka fiy nuhurihim, wa'a uzu bika min shururihim. Mu sani cewa Musulunci ya ummurce mu da mu tanadi makamin kare kanmu, kuma mu tunkari azzalumi da kabbara Allahu Akbar ! Tabbas tana jefa tsoro ga azzalumi kuma tana kara ma mutum karfin gwiwar tunkarar azzalumi.

Bamu fatar hakan ta kara faruwa amma in ta sake afkuwa don Allah Jibiyawa ku fito da makamin dake gareku Gora, Sanda, Takobi, Mashi da sauransu ku tunkari inda azzaluman nan suke da karfin gwiwar ku kamasu, in takasance kuka rasa rayuwarku To ba fa asara kuka yi ba, shahada ce, Ya Allah ka arzurtamu da shahada amin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post