Tare da Muhammad Rajab Muhammad
Babban burin 'yan mulkin mallaka shine mallakar manyan biranen da sune suka hada hancin daular musulunci anan kasar Hausa musamman Kano da sakkwato, ita Kano saboda itace cibiyar kasuwanci da tattalin arziki na waccan hamshaqiyar daula, domin haka turawa na kwadayinta sosai domin suna da cikakken labari akan karfin fada aji dana Soja da arziki domin kano itace ginshiki da take tallafar daular usmaniyya sannan alokaci guda turawa na tsoron samun matsala a kano domin idan wani tawaye mai karfi ya auku a can tofa dukka tufkarsu an warware ta kenan kamar yadda suke fada sun Taras da talakan kano yafi talakan dake birnin londan jindadi da yawan kudi a hannu a wancan lokaci.
Kuma sukace irin makaman yakin ciki kuwa harda bindigogi da suka taras a Kano a gaskiya ko mahadin Sudan da yayi musu tawaye ya wahalar dasu bashi dasu, haka na nufin idan yaki ya auku tsakaninsu da kano to matsala ta auku babba wacce tafi karfin ta Mahadin Sudan kuma aiki ya dawo musu baya kenan, Ita kuwa sakkwato itace cibiyar daular musulunci da tsare-tsaren mulki kuma dukkan sauran birane da garuruwa dake karkashin daular suna saurara mata uwa uba ma a can fadar jagoran daular take.
Domin haka itace tunga ta karshe da in kasami nasara akanta to shikenan ka mallaki daular da al'ummar kenan shiyasa ma LUGARD bai shelanta mulkin mallakarsa ba saida ya tabbatar ya mamaye sakkwato kuma ya kashe sarkin Musulmi Attahiru a garin bormi, to amma ya za'ayi kaci sakkwato da yaki Alhali kano na tsaye, kuma ya za'ayi ka cimma kano batare da kabi ta zariya ba.
Lokacin da LUGARD ya sami labarin magajin garin Keffi dan yamusa ya kashe kyaftin Maloney bai dauki abinda wasa ba domin yanada tabbacin kashe kyaftin moloney tamkar wata hanya ce ta bude musu na cimma wancan buri nasu na mamaye daular musulunci,haka lokacin da LUGARD ya sami labarin magaji dan yamusa ya gudu zariya yaji dadin wannan abu domin dama ta samu kenan na mamayar zazzau cikin hanzari LUGARD ya hada runduna mai karfi ta tunkari zariya..............MU HADU A KASHI NA UKU.
Tags:
Jagoran Gaskiya