Tare da Muhammad Rajab Muhammad
Muna yara a wajan 1979 cikin wani dare sojoji suka biyo wani dan'uwansu Soja har cikin anguwarmu suka ko rutsa dashi sukayi ta bugunsa had sai da yace ga garinku nan duk sunyi haka ne da sunan wai yayi musu sata a cikin bariki, Abu kamar wasa gari na wayewa sojoji suka mamaye unguwar suka shiga cin mutumcin mutane tare da kame na kan mai uwa da wabi, wadanda aka kama aka shigar dasu bariki, sun sha baqar wuya da tozarci kala kala duk wai da sunan zargin farar hular anguwa sun kashe Soja,aka kakaba mana dokar ta baci karfe 6:00 pm dole kowa ya shige gida duk Wanda yayi kuskure ya zarce wannan lokaci to wallahi ya Shiga uku da takurawa ta kai maqura jama'a suka shiga gudu daga wannan anguwa kafin wani lokaci gari ya zama kufai kowa yayi takansa.
Ni dinnan tare da 'yan'uwana muna daga cikin wadanda aka tasa keyarmu akayi hijira damu zuwa wani gari mai suna bomo a kasar zazzau can muka zauna wajen kakarmu mahaifitar babanmu har komi ya kwaranye, Wani abu data fito fili shine su sojoji sunyi niyyar kwace unguwar damancan suna ikirarin mallakinsu ce yanzu haka zasuyi amfani da wannan dama su hadeta da bariki, wannan yunkuri na sojoji ya gamu da ayar tambaya inda wasu me ganin damancan dalilin kashe wancan Soja shine Neman cika burinsu na mallakar wannan anguwa shine aka fake ma guzuma za a harbi karsana.
Lallai kam biri yayi kama da mutum domin menene ya gama kashe mutum daya da tashin gari baki daya da kuma kwace garin baki daya,Indai damar ba manufar ba kenan,wato a bata wa kare suna domin a sami daman rataye,Na kawo wannan kissar ce domin zata baka dama kayi tunani cewar shifa Wanda yake so ya zalunce ka to zai iyayin komi domin cimma muradinsa,gazawa daya da azzalumi me da ita.
Itace ta yaya zai aiwatar da zaluncinsa batare da angane zalunci yayi ba,shi yasa ako da yaushe yake Neman dalili dazai aiwatar da zaluncinsa batare da amfaci zalunci yayi ba bilhasali ma yanason ya sami damar da nunawa duniya Cewar Wanda aka zalunta ne azzalumi.
A waqi'ar data gabata ranar 12-12-2015 ranar da sojojin nijeriya 'yan ina da kisa suka kaiwa Harkar Musulunci a Nijeria karkashin jagorancin Sheikh Zakzaky (H) hari bisa zalunci an Shiga wani hali da takai ga wasu 'yan'uwa suna ganin yakamata Malam ya fita daga gyallesu domin sojojin nan dai da gaske suke shi suke hari, amsar da Malam (H) ya bayar ita ta kawo karshen wannan tunani inda Malam ya nunama 'yan'uwa a dogara ga Allah, kumama fitar ba itace zata kawo karshen harin nasu ba, bilhasali ma saima abinda zaici gaba.
'yanuwa sun fahimci matakin da Malam (H) ya dauka a matsayin shi ne mafita, Amma akwai wasu al'umma da suke ganin Yakamata da malam ya fita, tunda akwai damar yin hakan, bazan iya cewa komi akan masu irin wancan tunanin ba domin kowa da yadda yake kallon al'amari,to amma bari in baku wani labari Wanda zai bada dama ga duk masu irin wancan tunanin su watsar sannan sukai jinjina ga matakin da Malam (H) ya dauka Ku biyo ni.
KO LUGARD DA WANNAN DAMAR YAYI AMFANI YA KARASA RUGUZA DAULAR MUSULUNCI DA MUJADDIDI SHEHU USMAN DAN FODIO YA KAFA
Lokacinda magajin garin Keffi dan yamusa ya kashe baturen mulkin mallaka wani kyaftin na Soja na manta sunansa ,lugard ya bada umarni ga sojojinsa su Shiga Keffi su kamo masa dan yamusa da rai ko ba rai, wannan tasa dole dan yamusa yayi zabi daya ko hijira ko kuma Jan daga da turawa amma kasantuwarsa mai kula da karamar masarauta karkashin zazzau to ya zame mishi wajibi yayi hijira zuwa zazzau domin samun kariya wajen sarkin zazzau, To Ashe wannan mataki na dan yamusa yayima LUGARD dadi domin haka saida sukayi masa kofar rago ya samu ya fice daga garin Keffi da take yiwa magajin gari ya nufi zazzau. Ku biyo ni................... A KASHI NA BIYU

Tags:
Jagoran Gaskiya