Tare da Muhammad Rajab Muhammad
Duk da cewar magaji dan yamusa mafakar daya samu a zaria ,ba wata mai tsawo bace saboda wani dalili sai ya wuce kano, kuma tabbas LUGARD ya sami wannan labarin daga munafukansu amma bai hana su zo zaria Neman magaji dan yamusa ba da wata shirgegiyar runduna kuma nan take masarautar zazzau ta tabbatar musu dan yamusa yabar kasar zazzau,to amma abin mamaki wannan shigowar da sojojin mulkin mallaka sukayi da sunan Neman magajin garin Keffi dan yamusa shi ne kuma ya zame musu farkon mamaye kasar zazzau.
To kunga anan inda duniya da gaskiya tunda kun shigo gari Neman wani mutum kuka sami tabbacin ya fice, meya kamata suyi? shine suma saisu fice su tafi nemansa a gaba, to amma ina dayake lamarin nasu da manufa ai sai suka kara mike kafa bisa mamakin zage zage ma kawai sai kara ganin anata karo sojojin mulkin mallaka birnin nasu kafin wani lokaci cikin irin wannan hali na yaudara da LUGARD ya nuna tuni zazzau ta fada hannun 'yan mulkin mallaka.
Basu koma takan dan yamusa ba saida suka tabbatar Dari bisa Dari zazzau na hannunsu kai harma takai ga sun kama sarkin sunyi lokoja dashi a'inda helkwatar 'yan mulkin mallaka take,To yanzu burinsu na kame kasar zazzau ya cika, inane kuma burinsu na gaba? Kano, tuni na riga na fada muku cewar damar zaria itace tsaninsu ya zuwa kano, to gashi sun kamata batare da bata lokaci ba LUGARD ya hada wata kakkarfar runduna ta Soja Wanda saida takai yayo Karin sojoji daga Legas da Ghana, kada fa Ku manta suma zasu nufi kano ne da sunan kamo magajin garin Keffi dan yamusa haka ko akayi suka kama hanya suka tunkari kano da duk karfinsu.
A can birnin na dabo kuwa abinda ke faruwa shine sarki Alu ya karbi baquntar magajin garin Keffi dan yamusa kuma a daidai wannan lokacin a can sakkwato Allah yayiwa sarkin musulmi rasuwa kuma har an Nada sabon sarki wato sarkin musulmi Attahiru (1) kuma sarakunan daular suna ta ziyarar sakkwato domin ta'aziyya da kuma mubaya'a ga Sabon sarkin musulmi, to shima sarkin kano ba a barshi a bayaba nan take shima ya shirya ya kwashi tawaga ta fad'a dogarai da mayaka cikin kuwa harda magajin garin Keffi dan yamusa suka yiwa sakkwato tsinke..............MU HADU A KASHI NA HUDU.
Tags:
Jagoran Gaskiya