Labari Da Dumi Dumi



Zamu Kona Duk Wasu Kaya Da Suke Kan Iyakokinmu Matukar Najeriya Bata Bude Iyakarta Ba, Inji Kasashen Da Suke Makwabtaka Da Najeriya.
Daga Kabiru Ado Muh'd

Gwamnatin Kasashen Nijer, Chadi, da Kamaru da sauran kasashen dake makwabtaka da Najeriya sunyi barazanar kona duk wasu kaya da suke a jiye a iyakokinsu matukar gwamnatin Najeriya ba ta bude kan iyakarta ba.
Sunyi wannan furuci ne bayan fitowarsu daga wata ganawa da sukai isu isu kasashen.
Kasashen sun nuna damuwarsu ne akan cunkoson da suke fuskanta sakamakon tarin kayayyakin da suke jibge a iyakokinsu Wanda hakan ya haddasa komawar cunkoson har cikin garuruwansu dake kusa da iyakokin kasashen nasu.
Sun tabbatar da cewa nan da Dan wani lokaci matukar dai Najeriya ba ta bude iyakarta to tabbas zasu bada umarnin kona kayayyakin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post