Kullum jini ke Nasara Akan Takobi !!



-Ƙwarorin mutanen da basu kai ɗari ba mara sa kayan yaƙi da ababen hawa, aka shirya wa da mayaƙa da sukai dubu gomomi, dauke da makaman yaki da dawakai.

-Mutane da basu da yawa basu da kayan yaƙi akaiwa wanna shiri duk don neman bishe kiran Allah (T).

-Abinda ya faru a Karbala dama abu ne shiryayye da nufin ƙarar da masu kira zuwa ga Allah da iyalan gidan Manzon Allah (S).

-A nufinsu shine daga rana ta Karbala yazam komi na daga Saƙon Manzon Allah ya bishe, babu hanyar da zai kai ga wasu mutane.

-Amma abinda kullum jahilai keyi shike ƙara kambama kiran Allah a doron ƙasa, sunyi duk abinda zasuyi na ganin sunyi nasara amma hakan bai samu ba domin lamari ne na Allah.

-Bayan sun kashe yara da manya da marasa lafiya sai suke ganin sunyi, nasara alhali basu san wannan shine abin zaisa aita tunawa da abinda ya faru ba, a yabawa waɗanda suka sadaukar, a la'anci kuma makasansu kullu yaumin.

-Duba da Waƙi'ar Zaria zamuga cewa; daga wannan shekara da Waƙi'ar Zaria ya afku, yanzun mutanen da suka ƙara fahimtar addini ta dalilin hakan suna da yawan gaske, wanda da hakan bai faru ba ƙila da kiran baije garesu ba.

-Lallai, Allah yayi alkawarin kare addininsa koda kafirai da munafukai sunƙi, wannan waƙi'a data faru kuma ita ce sadaukarwar da Manzon Allah yayi da iyalan gidansa domin tabbatar addininsa.

-Badon Waƙi'ar Karbala ba, tabbas da bamu ƙara samun ƙarfin guiwa wajen bada rayukanmu wa addini ba, da shi kansa addinin baizo garemu ba.

-Faɗin Allah daya ke a cikin AlQurani mai girma cewa, "Bazaku hankalta ba" "Kuyi ta dabburi" wanna yasa in muka saka waɗannan a cikin fahimta ta hankali zai zama mun gane munyi tunani lallai, waƙi'ar Karbala darasi ce ga dukkan mumini mai neman yardar Allah.

-Matuƙar kana gabato da Waƙi'ar Karbala cikin ƙwaƙwalwarka bazaka taɓa samun santsin addini ba, kuma in muka ƙara kai tunaninmu ga abinda ya faru na Waƙi'ar Zaria zamu ga cewa; Allah yana sonmu kuma alamun ayyukanu suna kyau.

-Wannan yasa Allah ya gabato mana da Zaria Karbala domin mu ganta zahiri, ada muna jin labarin Waƙi'ar Karbala ne, sai Allah kuma ya kawo mana 'Photocopy' ɗin dukkan abinda ya faru a Karbala ɗin muma, don samun yaƙinin ayyukanmu, da samun damar sadaukarwa irin sadaukarwar sahabban Imam Husain (As) a ranar Waƙi'ar Karbala.

-Allah ya zabi Zakzaky a wannan Ƙarni, mu kuma ya saka mu cikin mabiyansa na haƙiƙa domin bashi kariya da kare addinin kakansa.

-Insha Allah kamar yadda ba'a kai ga sare kan Imam Husain ba saida aka ƙarar da dukkan Sahabbansa, muma Allah kayi amfani da jinananmu a wannan tafiya don tabbatar addinika, ka bamu ikon fansar ran Imam Zakzaky domin ganin ya cimma burinsa na ganin addinin nan ta tabbata a wannan Ƙasa dama Duniya baki ɗaya.

-Allah ya bawa su Sayyid (H) lafiya da nisan kwana, ya ƙwato mana su a hannun azzalumai cikin izza. Ilaheey

LABBAIKA YA RASULALLAH
LABBAIKA YA IMAM HUSAIN
LABBAIKA YA EL-ZAKZAKY

#FreeZakzaky
#FreeUmmahZeenat
#FreeAllMuslimUmmah
_____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post