Ko Kun Ki Ko Kunso Sai Musulunci ya Dago ya Mamaye Duniya !!


Cewar Sayyid Zakzaky (H)
Daga zauren Jawaban Sayyid Zakzaky (H)

Musuluncin nan ko kunki ko kunso sai ya dago kuma ya mamaye duniya munsan ma dai kunki din amman musuluncin nan Allah ya yarda dagowan zaiyi kuma sai ya mamaye duniya..
.
Wannan Manzo (s.a w.w.) sakon sa da akai qoqari a murguda sai al'ummah ta fahimce maye sakon kuma waye hakikanin wanann Manzon kuma mai yayi kira i zuwa gareshi ..
Wannan Manzon shine wanda yayi nasara akan makiyansa ba tare da yayi sara da takobi ba makiyan sa su suka je suka kai takobi
In har ya kare kansa a matsayin kare kai ne sai gashi ya fi karfin su ya shiga makkah da adadin da bazasu iya yaka ba suka fito suka daura hannuwan su a kyeyan su suna tsammanin duk fille musu wuya zai yi yace dasu mai kuke tsammani zan muku ?
Suka ce ai kai dan dangi ne kai mutum ne mai tausayi yace to ku tafi an yafe muku kuje na sake ku ku sakakkune.

Manzon Allah da kyakkyawan dabi'ar sane yayi nasara akan makiya bada yaki ba Manzon Allah ranzi ne na kyakykyawan dabi'a shi ne kamilin mutum in da akwai wanda zakace mishi PERFECT a mutane to shine , shine PERFECT,

sai dai a kwaikwaye shi shine samfur wanda Allah (T) ya aje don mu kwaikwaya .
To Har yanzu tunanin makiya shine su zasu i mana ne da karfin tsiya saboda koba komai sun san in aka zo babin hankali to mune zamuyi galaba to suna tunin kar asa hankali za ai fada ne a tsammanin su zasu galaba da fada din din to baza kuyi galaba da fadaba don a karken al'amari hankali ke nasara

wannan ko kunki ko kunso wannan manzo yana nan a samfur wanda ake kwafa da'awarsa na nan Daram
Wannan wani yanki ne na Jawabin da Sayyid Zakzaky (H) yayi a Ranar Maulud din Manzon Allah a Hussainiyyah 2015/1436

Aliyu Ibraheem Yarima

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post