Mun gaji da maimaita hujjojin halacci ko haramcin fadin “Happy Christmas”. Abin da ya kamata a yanzu shi ne mu yi amfani da wannan damar domin sanin wasu abubuwa na kwarai da zamu koya daga gurin Yesu Almasihu (as) a matsayin jagoran addinin da yafi kowane addini yawa a yanzu (Kiristanci) kuma Annabi daga cikin manyan Annabawan addinin Musulinci da ya fito daga cikin Yahudawa.
Kalmar Yesu ko Jesus itace take nufin Isa a harshen larabci. An haifi Yesu Almasihu a wani gari da ake kira #Nazareth wanda daga baya larabawa suke kira da “Nasara” kuma ya zama sunan addinin (ko darika daga darikun yahudanci) da ya zo da shi.
Kalmar Almasihu da larabci ta samo asali daga kalmar “messiah” da ma’anarta a turance take nufin mai kwato yanci ko mai assasa adalci; amma cikin asalin ma’anarta ta Hebrew tana nufin zababben Allah da ya shafeshi don ya kasance jagoran da zai kwatowa yahudawa yancinsu daga zalincin da suka dinga sha a hannun sarakunan Rumawa.
Da yake ba Annabi Isa ne kadai “Almasihu” ba a tarihin yahudawa, don an samu wadanda suka hau mukamin dayawa, kuma sunansa na “Jesus” ba sabo bane a cikinsu don an samu masu irin sunan da yawa, sai ya zamana an masa lakabi da sunan “Jesus of Nazareth” don a tantanceshi da sunan garinsu da a zamanin dan karamin kauyene da yake dauke da mutane yan tsiraru da basu fi daruruwa ba.
Tamkar kowane Annabi ko dan gwagwarmaya, Yesu Almasihu ya tashi ya tarar ana zalintar yahudawa karshen zalinci kuma kowane “messiah” idan yazo karshe kasheshi ake yi idan ya yi bore.
Shi nasa sai ya zamo kwato yanci ne amma ta hanyar son zaman lafiyar da har yake cewa dalibansa idan wani ya mareka to ka juya masa daya kuncin don ya mara ko don kada ya ji haushi.
To amma me ya janyo har yahudawan da yazo kwatowa yanci karshe suka yi yunkurin kasheshi ta hanyar gicciyewa?
Wannan yana da alaka da ganin da suke yi masa na cewa ya yi ridda ne saboda ya ce shi Annabi ne da Allah ya aiko. Yahudawa musamman mabiya darikar “Pharisee” sun tanka cewa ta yaya wanda ba dan sarauta ba kuma ba jikan Annabi Dawud ba zai zama Annabi kuma “messiah”! Su sun raina inda Annabi Isa din ya fito ne.
Su kam rumawa da suke yiwa Palestine mulkin mallaka a zamanin, a gunsu kalmar “messiah” tana nufin wani dan tawaye da yake son kifar da gwamnati.
Tamkar yadda kalmar “Shi’a” ko “Imam” ta zamarwa sarakunan Umayyah da Abbasiyya. Daga cikin gida ana ganinta da fuskar addini amma daga gurin masu mulki suna yi mata kallon kungiyar siyasa ta yan tawaye.
Annabi Isah ya fuskanci irin wadannan matsaloli guda biyu. Daga cikin gida yahudawa suna yi masa kallon wani batacce da ya yi da’awar Annabta alhalin bai gajeta ba, daga wajen sarakuna suna yi masa kallon dan tawaye.
#Merry_Christmas
Tags:
Munasabobi