So nake na Ankarar Da KU Abunda Qwaqwalwa ta Kasa Dauka
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
SO NAKE NA ANKARAR DA KU ABINDA QWAQWALWARKI TA KA SA RISKARSA
Shi karatu wani abu be dabam wanda mutane da dama kan yi shi amma sai su kasa daukar darasin da ke cikinsa, har sai an ankarar da su.
Za ka samu da yawa cikin malamai da ke karantarwa ba su san darusan da ke cikin karatun ba ballantana su nunawa dalibansu haqiqanin abinda karatun ke koyarwa.
Da yawan su sun karanta ayar da ke cew;
‘’ YAA KAI ANNABI ! KA FADAWA MATANKA DA 'YA'YANKA (mata)SU KUSANTAR DA TUFAFINSU (Hijab)ZUWA QASA......‘’.
Amma abin mamakin shine, shi malamin bai ma san cewa umarni ne na wajibi ba, a tsammaninsa labari kawai aka bayar, don haka ba ya aikata wannan umarni ballantana ya nunawa dalibansa cewa wannan umarni ne na wajibi.
Akwai hadisin Ma'aiki Allah(S.A.W.W)da ke cewa;
‘’ IDAN MACE TA SANYA TURARE HAR MAZAJEN DA BA MUHARRAMANTA BA SUKA JI (qanshin sa), TO, ALLAH BA ZAI KARBI SALLARTA NA TSAHON KWANA ARBA'IN (40)BA HAR SAI TA WANKE SHI BISA SON RANTA ‘’.
NAZARI
――――――
Idan muka nazarci wannan hadisi sannan muka auna shi da 80% na matan Ahlus-Sunnati za mu iya cewa sallar su ba ta karbuwa.
Hujjata ta wannan magana ita ce, babu mai qaryatawa cewa dukkansu sukan sanya turare yayin fitarsu zuwa gidan biki, asibiti, shago ko kuma dai zuwa ziyara.
Matan 'yan Shi'ah ne kadai ke yin aiki da wannan hadisi don kiyaye umarnin Allah da Ma'aikinsa (S.A.W.W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 9th Dec, 2019.