Tuna Baya:-Karanta Ganawar Wakilan Shafin Ma'asumah da Sheikh Ya'aKub Yahya Katsina !!!

Naji Dadi har Na zubar Da hawayen Farin Ciki


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
_____________________________

Yayin taron qarawa juna sani (MU'UTAMAR)wanda wakilan shafin Ma'asumah Nigerian News suka gabatar a garin Katsina kusan shekara guda kenan.

Munyi sa'ar ganawa da shi ta musamman don mu qara samun irshadi da sahihiyar fikira wacce Sayyid (H)ke shayar damu.

Bayan gabatar damu da aka yi daga wajen wani na kusa da shi, sai Shehun malamin ya buqaci kowa ya gabatar da kansa ta hanyar fadar sunansa da kuma garin da ya fito. Cikin ladabi da qasqantar da kai muka gabatar da kawukanmu.

Yayin dana ambaci cewa ni daga garin Ningi nake ta Jihar Bauchi, sai da Shehin malamin mai tsoron Allah a zahiri da badini ya fadi wata kalma kame da garin namu, wacce wannan furucin ya sanya ni yin murmushi kuma muka yi (smile sharing)tare da shi.


Yayin da ya fara yi mana nasiha kuwa kan tsoron Allah da kuma yin komai dominsa, tare da tsayawa kan haqiqanin koyarwar da Sayyid (H)ke yi mana, ban san lokacin da hawaye ya fara saukowa daga idanuwana ba, gaskiya na qara shaidawa cewa Sheikh Ya'aqub Yahya bawan Allah na gari wanda ake fatan kasancewa tare da irinsu a duniya da lahira.

Ya gargade mu kan cewa mu inganta aikinmu na Media ta hanyar tantance dukkan abubuwan da za mu watsa ga al'umma, labarai ne ko kuma wani ilimi . Ku ya qara gargadinmu kan cewa kada muci amanar Sayyid (H), mu kasance masu bin karantarwarsa har lokacin da Allah zai dawo da shi cikinmu. Har ma yake cewa;

" BABBAN BURINMU SHINE SAYYID (H)YA DAWO YA SAME MU KAN KOYARWAR DA YA BARMU A KANTA BA TARE DA MUN CI AMANARSA BA ".

Tun daga waccan lokaci na gara sallamawa al'amarinsa kan wanda nake da shi a baya.

YAA ALLAH KA BARMU TARE DA JAGORANMU SAYYID (H), DA KUMA QWATO MANA SHI DAGA HANNUN AZZALUMAI!

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 12th Dec, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post