Kafar sadarwa, kamar fagen daga ne da ake gwabza yaki!!

Nasiha zuwa ga masu ta'ammuli da kafafen sada zumunta......

Yanzun yakin da wasun mu suka dauka wa kansu a wannan kafa, shine aibata juna da nuna yan bangaranci, wanda ba haka manzon Allah (S) ya umurce mu ba, wannan sam ba koyarwarsa bace.

Yakama ta yakinmu a wannan fagen daga yazam yaki ne zuciya, mu yaki zuciyoyin mu da nushashshe da kawukanmu abinda ya shafi bauta wa mahiliccin mu da guje ma saba masa.  Mu kuma hada kan mu busa hanyar Allah kwar daya.

Kafar sadarwa yanzun wajene da babu kamar sa wajen isar da sako a fadin duniya, waje ne daya hada dukkan nin jinsi, al'ummu daban-daban.

Damuwar mu shine addini, kuma muna fatan yazam dukkan ayyukan mu mun damfaru da saka su akan hanyar addini, rayuwar mu baki daya yazam cikin tsantseni da sanin hukumcin addini a cikin lamuranmu.

To, a wannan yanayi da muke ciki, mun tsinci kanmu a wani lokaci da wasun mu bama su san ainihin dalilin zuwan su duniya ba, basu damu da addini ba, kai da kake kokarin ganin ka siffantu da addinin ma ana ganin kana kan bata ne.

Damuwar su shine abin duniya mai karewa, gani suke ma kamar baza'a koma ga Allah din ba, sabida idanun su ya rufe, domin ba a dora su kan hanya mikakkiya ba tun tasowa.

Ta wanne hanya zamu isar da sakon annabinmu da sauke hakkin sa akanmu? To, anan zan iya cewa hanyoyin suna da yawa amma, hanya mafi sauki itace kafar sada zumunta. Wajene da kowa keda damar tallata hajar sa, hajar nan kuwa kaso ka gani ko baka so in aka saka shi dole yazo gare ka. Domin yanayin da aka jefa kasar nan tamu aka barmu cikin talauci wasu abubuwan bazai yiwu maka yazam komi saika tara jama'a zaka sanar dasu ba.

Amam insha Allah, da raya munasabobin da muke danyi da sauran tunasarwa suma zasu bada gudun mawa sosai.

Mu hajar mu itace; addinin Allah da tabbatar da kiran Manzon Allah (S) ya shiga zuciyoyin dukkan al'umma. Domin sauke nauyin kiran al'umma, ba kamar yadda wasu ke fadin kasa daya al'umma daya babu banbancin addini ba.

Kasa daya Na'am amma tabbas ta wajen addini in baka kira mutane ba to, ran lahira zasu tuhume ka da baka nusasshe su ka ganar dasu hanya ta gaskiya ba, alhali kuma kai kasan suna kan bata din.

Abin takaici, mun maida rayuwar mu rayuwa mara tsari bawai kuma don bamu sani ba, a'ah saidai don mun dauki shagala da lalacewa mun biyewa banzayen dabi'u na turawan yamma makiya Allah, makiya addinin Allah(T), bamu damu da abinda yake gaban mu ba. Yawancin mu mun maida kafar sadarwa din nan wajen fira, in zakai fira da mutum ka karu daga irin iya mu'amalar sa ma 'Falillahil hamd' amma ina mai makon haka ma saidai kaji maganganu marasa kan gado, kuma a hakan dai mu kira kanmu ma'abota addini.

Mun dauka daraja da samun kusanci gurin Allah ana samun sa cikin sauki ne? Dole mu jajirce, mu maida abinda ake ganin bazai yiwu ba, ya yiwu kaji kai a rayuwa ma baka san wai wani abu da zaka saka a gaba kaji bazaka iya yinsa ba. Matukar ka rike Allah babu wani abu dazai zo maka wanda bazaka iya shiba.

Lallai, yakin mu, mu masu ta'ammuli da wadannan kafafen sadarwa shine amfani da alkalumanmu wajen tunatar da zaluncin azzaluma da kuma tunasarda mutane ainihin koyarwar addini na gaskiya. Hakan zai samu ne in mudin mun sha Ilimi, domin Sayyid (H) kullum abinda yake cewa matasan mu ayi karatu.

Domin saida ilimi ne ake samun kusanci zuwa ga Allah matukar dukkan abinda zamuyi, zamu ke tafiyar dashi irin na Amawa ne to, wallahi za'ai ta shan kunya ne. Ibada bai yiwu wa saida sanin ilimin ibada din, kada mu wukakanta kawukan mu da yin ayyuka kamar yadda muja ga wasu suna yi.

Hakika yana da gayar muhimmanci duk abinda kake kasan shi kasan hukun yinsa a addini.

Fatan Allah ya datar damu ya kara kimtsa mana ilimummukan sa cikin kwakwalenmu domin mu amfana, mu kuma amfanar da al'ummar da muke tare da su.

Alhamdulilah....

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post