ISAR DA SAKON ADDINI TARE DA DA'AWAR SHEIKH ZAKZAKY: Sheikh Yaqoub Yahaya Katsina Ya Fara Kutsawa Cikin 'Kauyuka.



Tare Da Ibrahim Yan Tandu

Kamar Yadda Tarihi Ya Tabbatar Cewa Duk Lokacin Da Mai Kira Zuwa Ga Allah Ya Tashi To Yana Samun Wasu Daga Cikin Almajiran Sa Da Yayima Tarbiya Su Rika Yad'a Da'awar Kota Hanyar Wa'azi Ko Mu'amala.Haka Kuma Idan Azzalumai Suka Kama Wannan Mai Kira Ko Mujaddadi To Almajiran Sa Ne Suke Cigaba Da Gabatar Da Wannan Da'awa Cikin Al'umma Kafin Ya Sami Faraj,Kamar Yadda Ta Faru Da Almajiran Imam Khomeini (QS).





To Muma a Wannan Zamanin Haka Abin Yake Tun Bayan Tashin Mujaddadin Wannan 'Karnin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky (H) Da Fara Da'awar Sa Zuwa Ga Addinin Allah, Almajiran Sa Wadanda Suka Kar6a Masa Tun Farko Suna Cikin Wadanda Yayima Tarbiya Tare Da Yad'a Da Da'awar Sa Ta Komawa Zuwa Ga Addinin Allah Tsantsarsa Wadanda Suke a Kusan Kowane Birni Da Kauye Domin Yad'a Wannan Kira Nasa.

Cikin Ikon Allah Tafiya Kuma Tayi Nisa Domin Kowa Tuni Azzalumai Suka Fara Aikin Nasu Na Kamu Da Kisa, Wanda Har Takaiga Anyima Mujaddadin Wannan 'Karni Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Kamu Kusan 10 Tare Da Kashe Dubban Almajiran Sa Ciki Kowa Harda 'Ya'yan 6 Maza Zalla, Shi Kuma Da Mai Dakin Sa Suna Kulle Hannun Azzalumai Kusan Yau Shekara 4 Kenan Cur Cikin Kasa Da Shekaru 40 Da Fara Da'awar Sa.

Bayan Kamun Wannan Mujaddadin Wasu Daga Cikin Almajiran Sa Sun Fantsama Neman 'Yancin Ta Hanyar Gwagwarmaya Tare Da Sadaukar Da Rai Da Dukiya Da Lokaci,Wasu Kuma Sun Shiga Neman Abinda Zasu Tallawa Masu Wancan Gwagwarmayar (Dukiya) Lokacin Da Wasu Kuma Tuni Sunyi Nisa Cikin Neman Ilimi Domin Cike Gurbin Wadanda Aka Kashe Cikin Dubban Almajiran Sa, Wasu Kuma Suna Cigaba Da Addu'o'i Tare Da Neman Tabbatuwar Dukkan Yan Uwa a Tafarkin Da Mujaddadin Ya Barsu Akan ta.

Lokacin Da Su Kuma Manyan Malamai Kuma Almajiran Sa Wadanda Sukayi Karatu Wajen Sa Kamar Su Sheikh Yaqoub Yahya Katsina Da Suka Rage a Raye Suka Fara Shiga Cikin Kauyukan Da Basu Da Masaniyar Addini Da Da'awar Mujaddadi Sheikh Ibrahim El-Zakzaky (H) Suka Fara Yad'a Da'awar Tare Kira Zuwa Ga Addinin Allah Da Abinda Ya Hau Kan Kowane Mutum Na Wajibi Tare Da Kira Zuwa Ga Tauhidi Ta Tarbiya Da Mu'amala Irin ta Addinin Musulunci Kamar Yadda Mujaddadi Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Yake Kira Domin Tsira Zuwa Ga Allah Gobe Kiyama.

Cikin Kauyukan Da Sheikh Yaqoub Yahaya Ya Fara Shiga Akwai Wasu Daga Cikin Karamar Hukumar Batagarawa Da Kuma Wasu Kauyukan Kananan Hukumin Jihar Katsina.

Allah Ya Karba Ya Kuma Cikama Mujaddadi Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Gurin Sa Na Ganin Tabbatar Addinin Musulunci a Nigeria.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post