Ina Malamai, da Masana na Duniya? Ina son A ganar Dani Abunda Wadannan Hadissan ke koyarwa !!!


Tayaya Zan girmama masu Cin Mutunci ga Annabi (S.a):???

TIR DA MUZANTA SHAKSIYYAR MANZON ALLAH (S.A.W.W)

Ba za ka taba jin irin wadannan kalamai na fitowa daga bakunan masoya Manzon Allah (S.A.W.W)ba, ko da kuwa sun fito daga wacce makaranta ce ta fahintar musulmi.
Irin wadannan kalamai na fitowa ne daga bakunan maqiya Manzon Allah (S.A.W.W)da suka qulla aniyar cin mutuncinsa da muzanta shi ta hanyar gurbataccen karatun su, wawaye kuma su gamsu da haka ba tare da yin amfani fa hankali ko ilimin da Allah ya ba su ba.
Wasu hadisai biyu (2)nake son kawowa cikin littafin wanda ba ya qarya a makarantar Ahlus-Sunnati (BUKHARI).

(1)- Adamu ya bamu labari yace, Shu'ubatu ya bamu labari daga A'amashu, daga baban Wa'ili, daga Huzaifata yace;
‘’ Manzon Allah (S.A.W.W)ya tafi makewayin wasu mutane, sai yayi fitsari a tsaye ! Sa'an nan yace a kawo masa ruwa, sai nazo masa da ruwan yayi alwala ‘’.
(Bukhari, hadisi na 224).

TAMBAYA
――――――
Shin, Annabi ne yazo ya ba shi labarin ko kuma shine ya fake yake leqensa?
(2)- Abdan ya bamu labari yace, Abdullahi Bn Mubaraki ya bamu labari yace; Amru Bn Maimun Al-Jazariy ya bamu labari, daga Sulaiman Bn Yasari, daga A'ishata tace;
‘’ NA KASANCE INA WANKE JANABA DAGA JIKIN TUFAFIN ANNABI (S.A.W.W), KUMA YA FITA ZUWA SALLAH TARE DA SAURAN RUWAN A JIKIN TUFAFIN NASA ‘’.
(Bukhari, hadisi na 229)
Ni dai na kasa fahintar haqiqanin darusan da ake son koyarwa mutane ta hanyar wadannan hadisai.

Wanda ke da amsa ya ganar damu ta hanyar ilimi ba ta hanyar jahilci ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 3rd December, 2019.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. MBismillahi, Was Salatu was Salamu Ala Rasulillah (S.A.A.W)!
    Bayan Haka, amsa ga mai tambaya:
    Hadisi na farko yana bayyana mana yadda kyakkyawar rayuwar Manzon Allah (S.A.A.W) take, a cikin dukkan al'amurra,hatta yin bawali, ko barci, ko makamantansu, domin muyi kyakkyawan koyi da Shi
    (لقد كان لكم فى رسول الله أسوة حسنه )

    Ba tozarci bane ga Annabi (S.A.A.W), Hadisai ingattattu suna nan masu bayanin yadda Annabi (S.A.A.W) Yayi bayani filla-filla, ba tare da 6oye wani al'amari na addini ba, tare da cewa Shine yafi kowa yawan kunya da hikimar zance.

    2.Hakanan Hadisin na 2, Aisha (Allah Ya kara Mata yarda tana amsa tambayar mai tambaya ne, domin irin ilmin da ta samu daga Annabi (S.A.A.W).
    A matsayinta na uwa ga dukkan muminai, amsar da ta bayar, ba rashin kunya bane, kuma ba tonon asirin Annabi bane, a'a bayar da amanar ilmi ne tayi.
    6oyewar ilmi shine laifi, kamar yadda Allah (SWT) Yace:
    إن الذين ينتمون ما أنزلنا من البينات و الهدى.....)أ

    ReplyDelete
Previous Post Next Post