Imanin Mu game da Badah.



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

  1     "BADAH  "ga Mutum'. Shi ne wani sabon ra'ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra'ayin ba, wato ya canja niyyarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi domin faruwar wani abu gareshi da zai sanya canji a ra'ayinsa da saninsa, sai ya canja niyya sai ya bar aikata shi bayan da can yana nufin ya aiwatar da shi, wannan kuwa ya faru ne sakamakon jahiltar maslaha da kuma yin nadama a kan abin da ya gabata. 

      "BADA" da wannan ma'anar mustahili ne ga Allah ( S.W.T ) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa. Wannan kuwa ya koru ga Ubangiji, kuma Shi'a Imamiyyah ba su yarda da shi ba. Imam Sadik ( A.S ) ya ce:

     " WANDA YA YI DA'AWAR CEWA CANJI CIKIN WANI ABU YA FARU GA ALLAH ( S.W.T ) GAME DA WANI ABU CANJI IRIN NA NADAMA, TO A GURINMU WANNAN YA KAFIRTA DA ALLAH MAI GIRMA." kuma ya ce:  " 
 WANDA YA RAYA CEWA WANI ABU NA CANJIN RA'AYI YA FARU GA ALLAH WANDA YA KASANCE BAI SAN SHI BA JIYA TO KA BARRANTA DAGA GARESHI."

Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamammu wadanda suke kusan nuni da ma'anar " BADA " kamar yadda ta gabata, kamar yadda ya zo daga Imam Sadik ( A.S ) cewa: WANI ABU BAI TABA BAYYANA BA GA ALLAH KAMAR YADDA YA BAYYANA GARE SHI GAME DA ISMA'ILA DANA. "

Dan haka ne wadansu daga Marubutan Musulmi na Ahlussunna suka danganta BADA ga Shi'a Imamiyya da waccan ma'ana domin suka ga Mazhabar Ahlul Baiti ( A.S ) suka sanya wannan daya daga cikin abubuwan da suke suka da aibata Shi'a da shi.

TARE DA ADAMU MUH'D NINGI

 Za mu ci gaba insha Allahu Ta'ala.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post