Imam Aliy (as) Ba Musulumta yayi ba, Yadai Jaddada Imanin Shi !!!


ANA MUSLIMTA NE BAYAN BAUTAR WANIN ALLAH

Abinda aka yi ittifaqi kansa cikin kowacce makaranta ta muslimci shine, hukunci na hawa kan wanda ya balagha (MUKALLAFI)ne. Sannan kuma kowa ya yarda da hadisin Annabi (S.A.W.W)da ke cewa;
‘’ DUKKAN ABIN HAIHUWA ANA HAIFARSA MUSULMI NE, SAI DAI IYAYENSA SU YAHUDANTAR DA SHI KO SU NASARANTAR DA SHI .‘’

Saboda haka tarihin muslimci ya tabbatar da cewa Imam Ali (A.S)tun yana qarami yake tare da Manzon Allah (S.A.W.W)cikin renonsa da tarbiyyarsa, sannan bai wuce shekara goma (10)ba aka aiko Annabi (S.A.W.W)a matsayin dan saqo, kuma Imam Ali (A.S)ya gaskata shi a ranar da Allah ya yayi masa wannan wahayi.

Ko da mutum bai yarda cewa an haifi Imam Ali (A.S)ya fado qasa yana sujadah ba, to, ba zai qaryata cewa bai bautawa wanin Allah (Gunki)ba, shi yasa ma shi kadai ne cikin Sahabbai ake ambatonsa da cewa (KARRAMALLAHU WAJHAHU).

Kuskure ne ko kuma rashin ilimi ka ji mutum na cewa wane ya muslimta, alhali dama shi musulmi ne. Ana ambaton cewa wane ya muslimta ne in har ya taba yin wani addini wanda ba muslimci ba.
Ya isa zama abin misali daga 'ya'yan musulmai a wannan zamani, ba za ka taba ji an ce yau yaron wane ya muslimta ba, menene dalili? Dalili shine da ma asalinsa musulmi ne.

Kuma da za a sami yaron arna wanda bai balagha ba ta fara sallah da koyon karatun alqur'an ba za a kira shi da sunan wanda ya muslimta ba, amma in wani ne daga cikin mahaifansa sai ace masa ya muslimta.
Asalin Imam Ali (A.S)musulmi ne kamar yadda ba za ka taba jin ance ga ranar da Manzon Allah (S.A.W.W)ya muslimta ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~ 2nd December,,2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post