Zakiru shine wanda ya riqi ambaton Allah a matsayin babban aikin sa, za ka gansu kowanne lokaci da CARBI a hannun su ko kuma rataye a wuyan su, kuma yawanci ana samun su ne cikin mabiya 'Dariqar Tijjaniyya.
Sunfi fifita wannan aiki fiye da komai, kuma ko da tafiya suke yi za kaga bakin su na motsi don ambaton Allah.
Abinda yake burgeni game dasu shine, za ka tarar dasu masu haquri da kuma juriya wajen wannan aiki nasu, domin za su iya shafe awanni bakwai (5hrs) ba tare da sun gajiya ba.
Daga cikin wasu masu da'awar muslimci suna ganin su tamkar mahaukata ne marar sa abin yi. Amma ni da naci karo da wasu hadisai sai naga ashe babban matsayi ne da su.
Iman Ahmad yace, Shu'aibu ya bamu labari, Ibn Wahab ya bamu labari daga Amru Bn Harith yace, lalle Darajan baban Samhu an ba shi labari daga baban Haisama, daga baban Sa'id Al-Khudniy yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" KU YAWAITA ZIKIRIN ALLAH MADAUKAKIN SARKI HAR SAI ANCE MUKA MAHAUKATA ."
" Faz-kurul-Laaha qiyaaman wa qu'uudan wa alah junubukum.....!"
(Ibn Kathir, J:3, Sh:542)
Shi kuma 'Dabaraniy cewa yayi, Abdullahi Bn Ahmad ya bamu labari, Uqbatu Bn Mukramul-Ummiy ya bamu labari, Sa'id Bn Safwan Al-Jahadariy ya bamu labari, Hassan Bn Abiy Ja'afar ya bamu labari daga Uqbatu Bn Abiy Shubaib Arrasibiy, daga Abiy Jauzaa'i daga Ibn Abbas (R.A) yace, Manzon Allah (S) yace;
" KUYI ZIKIRIN ALLAH IYA ZIKIRI, HAR MUNAFUKAI SUCE AI KU RIYA KUKE YI !"
(Ibn Khathir, J:3, Sh:543)
Daga nan na fahinci matsayin Zakirai, kuma nasan ashe munafukai ne ke ganin su mahaukata.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470