Idan har cutar da Mage zai zama sanadiyyar shiga wuta, to shi kisan Yan Shi'a a wane ma'auni yake ??


Wai Shin kisan 'Yan Shi'a Addini Ne ???

Idan har cutar da Mage zai zama sanadiyyar
shiga wuta, kyautatawa Kare zai zama
sanadiyyar shiga Aljanna a Musulinci, to shi kisan
yan Shi'a a wani ma'auni yake?

Addinin musulinci ya haramta cutar da makofta
koda ko suwane ne wandan nan makoftan, komin
yawan ibadan bawa idan yazama mai cutar da
makofta, wuta zaije ba da shakka ba, kamar
yadda ya inganta a Hadisai da dama, kuma shin
wai bisa kaddarawa, Shi'a kafurci ne, shin haka
Muslunci yake mu'amala da kafurai? Kuma shi
wannan mu'amalar da akeyi dasu shin bata
sunan Addini ne ko gyra shi? Shin kunaganin
Wanda ba musulmi ba zai yi sha'awar musulinci
da irin wannan tasarrufin da wasu masu da'awar
yada sunna sukeyi ga Wanda baya kan fahimtarsu? Shin Santana Qarar da Aqida da Qarfin
makami?

Kar kamanta! idan yau ka sama damar yin abinda
kakeyi da sunan Addini ko Sunna koma me
kabashi suna, ba zai dauwama ba, ita kanta
gwamnatin da kake takama cewa takuce ba zata
dauwama ba, kuma kasani ayyukan da kayi ayau
shine ake tarawa su zama tarihin rayuwar ka,
idan kai mai kyau tahinka ya zama mai kyau da
albarka, idan kai mara kyau tarihin ka ya baci,
kilama ta kaiga yan baya masu zuwa su rika
la'antar ka.

Addini dai shine kyawawan mu'amala
( ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﻌﺎﻣﻠﺔ )
Allah ya dawo damu cikin hayyacin mu

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post