Sheikh Zakzaky (H) a wajen Allah (T) yake kiran wannan al'umma da azo anemi mafita a wajensa, da ace akwai wata hanya wadda idan anbi za'a fita, da Sheikh Zakzaky (H) tuntuni yayi bayaninta, to amma babu wannan hanyar, ita kenan wadda yake kira azo abi!"
Mutane musamman na wannan kasa dana wannan nahiya akwai hakkin Sheikh Zakzaky (H) a kanku, shi dai nasa akanmu yagama sauke mana, yayi kira yarage ma mutum ya karba ko kar ya karba ruwansa, wannan kira da wannan bawan Allah yake shine mafitar duk wani mumini, duk mutuminda kaga yana kiyayya dashi to kabinciki imaninsa da walakin goro cikin miya!.
Idan akaje lahira akazo kan hakkin sauke nauyin da yarataya ga wanda yasan hanyar kira, idan akazo kan Sheikh Zakzaky (H) shifa yanada amsa' cewa ya kira, to idan akazo kan al'umma fa' idan aka tambaya kun amsa? wace amsa wannan al'umma take da'ita?
Idan kana ganin ai shi maikiran baiyi daidai da mazhabar dakake tafiya ba, ko kuma ba wanda kakeso bane, to kai kayi tawaye mana kayi bara'a mana, kanemi maceci kayi masa bai'a mana a'irin tafiyarda kekeso!.
Wannan bawan Allah tafiyarsa akwai gaskiya, kuma yana daga cikin dalilin dayasa mufa bazamu bar maganarsa ba, koda kuwa za'ayi mana abinda akayi masa, munyarda mutsira a lahira, mu fuskanci kalu balae a wannan duniyar!.
Q
Allah (T) katausaya mana da fitowar Jagoranmu Sheikh Zakzaky (H) Allah (T) kasaka mana zaluncinda akayi mana, Allah (T) kayi mana taimako, Allah (T) kakarfafi Yan'uwa, Allah (T) ka'amfanardamu!.
Tags:
Jagoran Gaskiya