TAMBAYA:- Idan mutum ya zauna cikin janaba (saboda wasu dalilai) har aka kira sallar asuba, to, shin ya halatta yayi azumi a wannan rana?
AMSA:- Babu wata matsala ga azuminsa idan dai azumin ba na Ramadan ko ramuwarsa bane. To, amma a azumin Ramadan ko ramuwarsa, idan har ba zai iya wanka ba, to, dole ne yayi taimama, idan kuma ya bar taimama, to, azuminsa ba ya inganta.
TAMBAYA:- Idan yayi azumi na wasu ranaku alhali yana cikin janaba, ba tare da ya san cewa tsarki daga janaba yana daga cikin sharadin azumi ba, to, shin wajibi ne ya yi kaffarar wadannan ranakun da ya yi azumi a cikin su da janaba, ko kuma ramakon su kawai ya wadatar?
AMSA:- Idan mutum ya wayi gari da janaba alhali yana sane da cewa yana da janaba, amma ya jahilci wajibcin yin wanka ko taimama (kafin ketowar Alfijr), to, wajibi ne a gare shi bisa Ihtiyadi yayi kaffara bayan ramako, sai dai idan jahilcin nasa ba a sakacinsa bane, to, anan ba wajibi bane ya yi kaffara, ko da yake Ihtiyadi ne yin kaffarar.
(Ilimi da tsarki sai gidan Annabta) !
Za mu cigaba insha Allah.
Tare da Ado Isah Guda.
Tags:
Tunatarwa