-Mace Musulma da Namiji Musulmi mai imani dole ya kiyaye kallonsa.
-Domin babu wanda aka yarje masa kallon ɗayan bangaren jinsinsa ba tare da ɗayan ɓangaren ya zamana Muharraminsa ba.
-Kamar yadda Namiji yake yaƙin nemarwa kansa da iyalinsa hanyar rayuwa mai ƙyau ba'a buƙaci daya rufe dukkan ilahirin jikinsa ba, saidai bisa wani dalili.
-Hakan bai kuma bashi damar ya tsananta kallonsa ga macen da ba muharramar sa ba.
-Ita Mace kuma anso ta lulluɓe ilahirin jikinta da keɓancewa a wajenda baza'a ke ganinta ba.
-Domin ita dukkan wani sashi na jikinta Al'aura ce, wannan yasa aka umurceta da ta rufe kanta, kuma ta kiyaye kallon Mazajen da ba muharramata ba.
-Kamar yadda aka ruwaito a hadisai masu inganci....
"Kallo kibiya ne mai guba daga kibiyoyin Shaiɗan"
"Ku kiyaye yawan kallo, sabida yawan kallo kan jawo matsananciyar sha'awar wanda ake kallo"
-A wani hadisin kuma an ruwaito Manzon Allah (S) yace, "Duk wanda ya cika idanunsa da kallon mace ba bisa kallo na shari'a ba, Allah zai tasheshi a ranar alƙiyama da ƙusoshi na wuta caccake a cikin idanunsa , har sai an gama yiwa kowa hisabi, sannan za'a umurci da a wuce dashi masaukinsa a gidan wuta"
-Hadisai sun tabbatar cewa; Kallo baya ga kallom farko kibiya ne na Shaiɗan, kuma haramun ne, mazanmu da matanmu mu ƙara tunani akan wannan hadisai, domin mu gane saka Hijab bashi ke bawa mutum damar kallo ba bisa ƙa'ida ba ga abinda yake na Haram.
Waiyazu Billah......
____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
.