Ci gaban rubutun Hijabi...
Zamuyi magana akan waɗansu abubuwa.
RUFE DUKKAN JIKIN MACE
-Tufafi dole ya rufe dukkan jiki, saidai waɗansu wajaje keɓantattu. Da aka kawo a cikin ingantattun hadisai na Shi'a da Sunnah. "Dukkan mace al'aura ce".
-Menene ma'anar al'aura? Amsar anan itace; Boyayyun gurare al'aura ne su, sabida abin kunya ne mutum ya kallesu ko bayyana su: kuma dukkan abinda namiji yake ɓoyewa sabida kunya ko su ababen alfaharinsa ne su ake kira al'aura "Awra", kuma mata su dukkan jininsu al'aura ne.
-Bisa Urwatul Wuthqa daga Sayyid Khazim Yazdi ya nuna ra'ayinsa akan rufe jiki sun kasu bisa kaso biyu.
1- Rufewa na wajibi a ko wanni lokaci da manufarsa.
-Rufe al'aura (zahirinsa da baɗininsa) daga ko wanni mutum mace ko namiji, muharrami koba muharrami ba, balagage ko ba balagagge ba.
-Saidai: Miji da mata zasu iya kallon juna, da kuma ƙaramin yaro shima ba matsala ga hakan.
-Kamar yadda yake haram ga kowa ya kalli waɗannan wurare, hakama haramun ne ka buɗesu.
-Wajibi ne ga mace da rufe dukkan jikinta, banda fiskasta da tafukan hannunta. Amma baya ga mijinta.
Fiska da Hannu
-Idan da yiwuwar wani yaganta da matsananciyar sha'awa, wajibi ta rufe hannunta shima.
-Idan babu yiwuwar hakan ba wajibi bane ta rufe su dangane da Fatawar Sayyid Khazim Yazdi, Sayyid Muhsin Hakim Tabataba'e, Sayyid Mahmoud Husaini Shahrudi, Sayyid Abul-Qasim Khui, Sayyid Muhammad Khazim Shari'adari, Sayyid Muhammad Ridha Gulpayegani da Sayyid Hadi Milani.
-Haram ne kai kallo da matsanancin sha'awa ga jiki, fiska da hannun namiji ko mace, shiɗin muharraminka ne koba muharraminka ba. Saidai: Miji da Mata