Harma Ankaimu Kotu akan Wannan...!!!


_______Jibril Usman Sarki
“Har ma an kaimu kotu akan wannan, a lokacin Abacha, su suna cewa, wai daga cikin mu, wai muna gaba da gwamnati? Sai nace ai wannan bashi da ma'ana, kace kana gaba da gwamnati, nace wannan rubbish ne, nonsense, saboda duk inda ka samu society, tana da gwamnati, in ba haka ba, za a zauna a kiosk kenan, an zama dabbobi kenan, dole ne ya zama akwai gwamnati.
Da ma kun ce muna adawa da wadansu policies na Janaral Abacha, sai judging yace kar ka fa daure kanka, sai nace ai nasan abinda nake fada, ba daure kaina nake yi ba.
Yana cewa, don’t hook your self, nace nasan abin da nake fadi, abin da nake nufi shi ne, dole ne a kowace al'umma akwai gwamnati, ba yadda za ayi kace kana adawa da gwamnati, ba shi da ma'ana. Sai dai kace wane policies din sa, baka yarda da shi ba, to sai yayi ma'ana. Amma ba gwamnati ba. Su a gurin su gwamnatin ne kawai ake cewa, wato a zauna ba hukuma kenan? a zauna kara zube, ba gwamnati kenan? an zama dabbobi kenan.

Don Dabbobi ne basu da gwamnati, sai a tatsuniya. Za ka ji an ce Zaki shi ne Sarki, ai ba haka bane. Ka je dajin ka gani, in za kaga Titunan da gwamnatin tayi da jami'an tsaron ta, da sauran su, zaka ga ana kara zube. Ba yadda za a yi a ce, wai mutum yana adawa da gwamnati ne, sai dai in mahaukaci ne, don hauka kenan.

Ni ina fadan, abin da mutane suke cewa, wai mu muke cewa ne, to shikenan, sai suka yi ta fadan wai gwamnati, gwamnati, gwamnati. Wai ana fada da gwamnati, wato gwamnati far say kenan”

Kadan daga Jawabin  Shaikh Ibraheem Zakzaky, a Mu’utamar din da Academic Forum da Sisters Forum suka shirya a Katsina, 2013.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post