Zamanin jahiliyya mata sun fiskanci rayuwar bakin ciki, kunci da barazanar mutuwa ko wanni lokaci.
Don haka mata basu da wata daraja, basu da wani matsayi balle ake girmma su ko basu hakkokinsu, hasali ma kashe su ake da ransu tun suna jarirai. Wai a cewarsu; "Yawan haifar mata zai haifarda rugujewar tattalin arzikin su".
Wannan abin bakin ciki da nuna alhini ne musamman ga mutane masu tausayi da imani, abinda kawai suke kira da amfanin mace a wannan zamani shine: samar da 'ya'ya musamman 'ya'ya maza, girka abinci da wanke kaya.
Babban abin takaici mata rashin 'yancin su yakai har da yakan iya gadon mahaifiyar, kanwarsa ko kishiyar maman sa kuma yake tara wa dasu a makwanci daya in mahaifin sa ya rasu.
Barna tayi yawa bana manta wa Malam Zakzaky (H) yake cewa; "Akwai wani sahabi cikin sahabbai shi kadai in ya tuna abinda yayi a baya saiya kama kuka, domin yakan yawan tuna abinda yayi wa diyar sa ta cikinsa, yayin da yaje bisne ta yana haka ramin amma itake share mai zufa, amma da ya gama hakan baisa yaji tausayin ta ba da karfi ya turbuqa ta ciki ya rufe". Wa'iyazu billah.
A wannan lokaci mata kusan tsirara suke tafiya, saidai manyan mata kamar irin matan masarautar Byzantine da Masarautar Persia suke saka dan abin rufa jiki kamar haka👇
Zuwan Annabi Muhammad (S) da annabta shiya cenza komi, da Umurnin Allah (T) Manzon sa cikin hadisan sa bai gushe ba yana bama mata hakkin su da nusashe da mutane akan hakkokin mata da yadda za'a bauta wa Allah domin tsira ranar tsaiwa.
Allah yake fada wa Manzon Allah (S) kamar yadda yazo a cikin Qurani mai girma, "Ya Ma'aikin Allah! Ka umurci matanka, yayanka da matayen mu'minai, su rufe tsiraicin su da tufafi daga mutanen da ba muharraman su ba, Allah mai yafiya ne kuma mai jin kai."
Suratul Ahzab, aya ta 59.
Wadannan wajen da Manzon Allah yake bayani akansu su ake kira 'Al'aura' domin su mata dukkan jikin su al'aura ne, banda tafikan hannun su da fiskokin su, a wasu wajen ma sukan su tafika da fiskan akan rufe su in yazam zasu haifar wa wasu fada wa ga halaka.
A wannan lokaci da muke ciki in badon yazo a cikin Qurani da hadisan Manzon Allah (S) ba in aka fada wa wasu matan zasu dauka karya ne, domin yanzun mata sun sami 'yanci, walwala da kuma ingantattar kariya daga addini Musulunci. Hakika, Muslunci rahma ne ba wata mace ko namiji da zai sami 'yanci fiye da 'yancin da Muslunci ya bamu.
Da wannan nake kiran Iyayenmu, 'yan uwanmu da kuma kannen mu mata dasu kai duba ga halin da a wannan zamanin mata suka tsinci kansu su danganta da wannan lokaci da suka sami 'yanci ko sa samu damar bauta wa Allah bisa wannan babbar ni'ima da yayi mana, ni'imar Muslunci.
Su kula da mazajen su, domin ta hanyar su ne zasu kai ga samun tsira a ranar Alkiyama....
Allah ya datar damu ya kara bamu ikon bauta masa da iklasi.
Daga
Bin Haroun Sigau
08065008703
Tags:
Muhimman zantuka