Ha ha ha ! Abu Huraira da Abun dariya kake


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Sau da yawa, idan ina sauraron karatu/wa'azin malamai sai na ji suna kawo magana ta barkwance wacce ke sa masu saurare su yi dariya. Shine nake cewa ko da ma daga irin wannan barkwance na Abu Huraira su ka samo?
Ya kawo abin ban dariyar nasa ne cikin wani hadisi da ke magana kan falalar ciyar da iyali.

Bukhari yace; Umar Bn Hafsi ya bamu labari, babana ya bamu labari, A'amashu ya bamu labari, baban Salih ya bamu labari yace; Abu Huraira ya bani labari yace, Annabi (S.A.W.W) yace;
" MAFIFICIYAR SADAQA ITA CE WACCE AKA BAR MAWADATA (aka bawa raunana), KUMA HANNUN SAMA (na bayarwa) YA FI HANNUN QASA (me karba) ALKHAIRI, KA FARA DANA SAMA (me bayarwa ."

Mata (wife) na cewa; " KO DAI KA CIYAR DANI KO KUMA KA SAKENI ."

Bawa (slave) kuma na cewa; " KA CIYAR DA NI KUMA KA BANI AIKI."

'Da (son) kuma na cewa; " KA CIYAR DA NI ZUWA GA WANDA KE KIRANA (Allah) "

Sai (masu sauraronsa) suka ce; " Yaa Abu Huraira ! Daga Manzon Allah (S A W W) kuwa ka ji wannan magana?" Yace;
" A'A, WANNAN DAGA BARKWANCEN ABU HURAIRA NE ."
(Bukhari, hadisi na 5355)
DARASI
____________
Abinda gundarin hadisin ke karantar damu shine, mafi girman ladan sadaqa da za kayi ita ce wacce za ka bawa raunana mabuqata, ba ka qarawa me qarfi qarfi ba.
Sannan kuma ka kasance mai bayarwa (yin kyauta) ba wai ka kasance ko da yaushe sai dai a baka ba, yin hakan qasqanci ne da qarancin samun alkhairi.

Abinda Abu Huraira kuma ke nunawa cikin barkwancen nasa shine;
Ita mace 'yar tawaye ce.

Bawa kuma mai biyayya ne, amma fa yana so ka riqa qosar da shi.
Shi kuma da (son), me neman haqqinsa ne b daga mahaifansa, wato a ilmantar da shi da kuma tarbiyyantar da shi kan abinda zai kyautata alaqarsa ga Allah.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post