-Cewar Gwamnatin Nijeriya "Al-Zakzaky shugaban Harkar Muslunci so yake ya Musluntar da Nijeriya"
-Ko menene abinda mutanen Nijeriya suka fahimta dangane da wannan maganar?. Wannan abu ne mai muhimmanci da za'ai nazari akai. Amma sai naga ko in kula a kewa maganar amma lallai, abu ne mai ma'ana duk da cewan ƴan Nijeriya in suka ji an danganta maganar da komawa hanyar adddini irin na Iran.
-Abin duban shine menene addini? Kuma taya za'a gudanar da rayuwa bayan kafuwar addinin?, a saninmu addinin Allah kwara daya kuma Allah yake faɗa cikkn AlQu'ani mai girma, "Ban halicci mutum da Aljan ba saidon su bauta min".
- LatsaWannan Vedion Domin ganin want jawabi na makircin Da Sherk Al'Zakzaky ke fallasawa.
-In mukai duba da maganar Addini zamuga Muslunci addini ne dake bawa kowa ƴancin rayuwa mai inganci, Musulmi ne, Krista ne, ko dabba ne, ko wanne zaka gan addinin nan ya nuna mana yadda za'a tafiya da rayuwarsa ta yadda zai sami rayuwa mai inganci, da tausasawa.
-In mukai duba ga Jamhurriyar Muslunci ta Iran zamuga cewa; kasace da ta haɗa Musulmai, Shi'a da Sunnah, Kristoci dama
wasu sauran addinai, amma in ka bincika zaka ga kowa yana da ƴanci da damar bauta iya fahimtarsa. Kamar haka ma a wannan Ƙasa muke burin haka ya tabbata, domin ƴantar da dukkan ɗan Adam da komi dake rayuwa a wannan Ƙasa tamu, domin ciƙa aƙƙawuran da muka ɗauka na bautawa Allah.
-Amma sai mutane suka jahilci wannan Kira ta Sheikh Ibraheem El-Zakzaky (H), wanda hakan yake ƙara bawa azzaluman mahukunta dama da ƙarin ƙarfin mulkan mutane cikin zalunci da danniya, waɗansu har suke ganin sune ma Allah yace ayiwa biyayya.
-A tunaninsu cewa wai ba'a faɗa da gwamnati, duk tsoronsu akan mutuwa ne, sun manta da a aikin banza ma akan mutu, ƴan boko haram da "Kidnapper" izina ne akan mu, ya rage naka ka mutu akan addini ko a karin banza tare da rasa cikar burikan da ka ɗeboba, da kuma samun sauke uzuri.
-Lallai, yana da gayar muhimmanci mutane suyi koyi da irin tafiyar magabatanmu dangane da saɗaukarwa da bawa addini kariya tako wanni fanni, koda ko za'a gididdiba ka, matuƙar akan addini ne hakan ya faru dakai baka da wata danasani.
-Domin in muka kalli Annabawa da sauran manyan bayin Allah masu tajdidin addini, zamu ga ba wani wanda yazo yana kira a koma ga addini ba tare da ya fiskanci jarabawoyi, kisa da ɗauri da musgunawa daga shugabannin gargajiya da sauran al'umma ba, addini fa! Ba ana yinsa ne ba tare da fiskantar jarabawa ba, a'a jarabawarma gwaji ne na imanin mutum.
-Sunnar addini ne wannan domin haka muyi da ƙoƙarin fiskantar dukkan abinda muka san dama dole zai faru, matuƙar munyi riƙo da hanyar Allah miƙaƙƙiya. Kar ya zam tunanin jin daɗin duniya ya rinjayi zuciyoyinmu mu kasa bin hanyar addini na gaskiya, in mukai haka zai zama ranar lahira bamu da hujnar bawa Allah, domin yayi mana dukkan ni'ima kuma ya futar mana da ƴan aikensa waɗanda zasu sakamu a hanya.
-Malam Zakzaky a wani jawabi nasa yake cewa, "Mu wannan harka munayi ne don sauke haƙƙin Allah da neman yardarsa"
SHARHI
.............
-Basai nace komi akan abin da ya faru ko ince ke faruwa da Sheikh Zakzaky ba, ya isa hujjah mu gane shifa! Ba damuwarsa kansa ba, a'a damuwarsa shine ƴancin al'umma da komawa zuwa ga addini na gaskiya.
-Da yawan lokuta gwamnatin nan garin neman su tozarta Harka Islamiyya sai jahilcinsu ya kaisu ga kambamata zuwa wajen da bata kai ba, yanzun kiran Malam Zakzaky (H) ba iya Nijeriya kawai ba, duk duniya tana sane da shi, da cin zarafin da ake mana, bugu da ƙari nema mana ƴanci.
-Don haka yanzun muka fara kira zuwa ga addini kuyi abinda zakuyi, mu Allah muke tsoro wutarsa ce abin gudunmu, kuma muna da tabbacin baku da abinda zaku iya yi mana face sai Allah ya so, shine mai iko kan komi.
ALLAH YA TABBATAR DAMU YA ƘWATO MANA SU SAYYID (H) CIKIN IZZA DA KOSHIN LAFIYA.
#FreeZakzaky
#FreeUmmahZeenat
_____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
Tags:
Jagoran Gaskiya