FIFITA SAHABI A KAN MANZON ALLAH (S.A.W.W) ! ! !


ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻭﺣﺒﻴﺒﻨﺎ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻘﺎﺳﻢ ﺍﻟﻤﺼﻄﻔﻰ
ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﺍﻟﻄﻴﺒﻴﻦ ﺍﻟﻄﺎﻫﺮﻳﻦ ﺍﻟﻤﻌﺼﻮﻣﻴﻦ .
Allah ta'ala ya shaidi Manzon Sa Muhammad
(A.S) Cikin Suratun Najmi Aya ta 3-4, In da ya ke
cewa:
ﻭَﻣَﺎ ﻳَﻨﻄِﻖُ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻬَﻮَﻯ
ﺇِﻥْ ﻫُﻮَ ﺇِﻟَّﺎ ﻭَﺣْﻲٌ ﻳُﻮﺣَﻰ

Ma'ana:
Kuma baya Magana da Son Zuciyar Sa.
Maganar Sa bata zamo ba, Face Wahayi ne da
ake aikowa.

Wadannan ayoyin 2, suna tabbatar mana da
Manzon Allah (S.A.W.W) Ma'asumi ne ta
kowanne bangare kuma ba zai yi umurni akan
rashin sani ko dagangan ba. Don haka ne ma
Allah ya umurci Muminai da su yi masa (Manzon
Allah) cikakkiyar biyayya akan duk wani umurni
da ya umurcesu dashi ko barin abin da ya
hanesu a kai. Kamar yadda yazo cikin Suratul
Hashar Aya ta 7, cewa:
ﻭَﻣَﺎ ﺁﺗَﺎﻛُﻢُ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝُ ﻓَﺨُﺬُﻭﻩُ ﻭَﻣَﺎ ﻧَﻬَﺎﻛُﻢْ ﻋَﻨْﻪُ ﻓَﺎﻧْﺘَﻬُﻮﺍ
Ma'ana:
Kuma duk abin da Manzon Allah yazo maku dashi
to ku karbe shi, Wanda kuwa ya haneku akan shi
ku gujeshi.

Wannan ayar itace ke tabbatar mana da mika
wuya kai tsaye ga umurnin Manzon Allah
(S.A.W.W) da watsi ga abin da yayi hani akan
shi, koda kuwa a wajan Muminai suna ganin haka
abin yake.

Amma zaka sha mamakin yadda littafan
Wahabiyawa suka cika da nuna Fifikon Sahabi
akan Manzon Allah (S), suna kaskantar da wanda
Allah yaiwa shaida don kare sahabi. Nuna fifikon
wani sama da Manzon Allah (S) koma waye
wannan shine ake kira "SHISH'SHIGI " a
Musulunci kuma hakan babban zunubi ne da ke kai mutum ga halaka duniya da lahira.

Shahararran Malamin Wahabiyawa, Muhammad
bin Abdullahi bin Abdul Latif Aljurdani a cikin
littafinSa (Misbahuz Zulam) Juzu'i na 2, Shafi na
25, ya kawo wata ruwayar Shish-shigi da ke nuna ffifikonKhalifa Abubakar akan Manzon Allah (A.S). ruwayar tazo kamar haka:
ﺃﻥ ﺭﺟﻼًًً ﻣﺎﺕ ﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺄﺭﺍﺩ ﺍﻟﻨﺒﻲ ‏( ﺹ ‏) : ﺇﻥ ﻳﺼﻠﻲ
ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻨﺰﻝ ﺟﺒﺮﻳﻞ ﻭﻗﺎﻝ : ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻻ ﺗﺼﻞ ﻋﻠﻴﻪ ،
ﻓﺈﻣﺘﻨﻊ ، ﻓﺠﺎﺀ ﺃﺑﻮﺑﻜﺮ ﻓﻘﺎﻝ : ﻳﺎ ﻧﺒﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻤﺎ
ﻋﻠﻤﺖ ﻣﻨﻪ ﺇﻻّ ﺧﻴﺮﺍًًً ، ﻓﻨﺰﻝ ﺟﺒﺮﻳﻞ ﻭﻗﺎﻝ : ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻞ
ﻋﻠﻴﻪ ، ﻓﺈﻥ ﺷﻬﺎﺩﺓ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻣﻘﺪﻣﺔ ﻋﻠﻰ ﺷﻬﺎﺩﺗﻲ .
Ma'ana:
Wani Mutum ya mutu a cikin madina sai Manzon
Allah (S) ya yi niyyar yi masa Sallah, sai Mala'ika
Jibrilu ya sauka ya ce da Annabi: ''Yaa kai
Muhammad!! kada kayi masa Sallah,'' Sai Annabi
ya bari! Abubakar ya zo ya ce: ''Yaa Annabin
Allah!! bansan komai akan wannan mutumin ba
sai alkhairi'' Sai Jibrilu ya kara sauka ya ce da
Annabi: ''Yaa Muhammad ka Sallace shi, Saboda
Shaidar Abubakar tana gaba da Shaidata.''
Wannan kadan kenan daga irin matsayin da
Wahabiyawa ke ba Sahabbai. Sun kasance suna
daukaka matsayin Sahabi sama da Manzon Allah
(S) kamar yadda muka gani cikin ruwayar data
gabata daga littafin su. Zamu iya cewa ruwayar
na bayyana mana cewa:
-Manzon Allah baisan gaibu ba shiyasa yabi
umrnin Mala'ika Jibrilu na dakatar da Sallatar
mutumin.

-Ayar da Allah ke nuna mala'ika yana gabatar da
umurnin Allah ne ba gaskiya bace domin ya yi hhania farko sai ya koma yayi umurni sakamakon
shaidar Abubakar ga Mutumin.
-Abubakar nada ilimin da Manzon Allah bai sani
ba kuma yafi Mala'ika Jibrilu Ilimi da daraja.

Wadannan Nuq'do'din (Points) suna da
muhimmancin gaske da zamu iya fahimtar
Addinin Wahabiyanci ya ginune akan Fifita
Sahabbai sama da Manzon Allah (A.S).
Muna rokon Allah Ya yi mana tsari da irin
wannan fikira ta daukaka wani Sahabi sama da
Annabi Muhammad (A.S).

ﻓَﺒَﺸِّﺮْ ﻋِﺒَﺎﺩِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﺴْﺘَﻤِﻌُﻮﻥَ ﺍﻟْﻘَﻮْﻝَ ﻓَﻴَﺘَّﺒِﻌُﻮﻥَ ﺃَﺣْﺴَﻨَﻪُ
ﺃُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫَﺪَﺍﻫُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﺃُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﻫُﻢْ ﺃُﻭْﻟُﻮﺍ ﺍﻟْﺄَﻟْﺐَ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post