FADAKARWA ZUWA GA AL'UMMAH


Ya kamata idon Iyaye da Al'umma da Mahukunta da Malaman Addinin Musulunci ya kai kan wanna Mummunan Al'adar da ake yayi yanzu. Wacce idan an kammala makarantun gaba da sakandare akeyi.

Kamar yadda ake gani a hoto, wannan shi ake kira da (Sign-Out) wata Al'ada ce da Samari da 'Yan mata suke cudanya ta hanyar tattaba sassan jikinsu da nufin alamta rubutun ban kwanan rabuwa a Makaranta.

A yayin gudanar da wannnan bakuwar Al'ada akwai abubuwa marasa kyau da akeyi, kamar:-

Rashin kunya, Almubazzaranci, Fasikanci, Haramtacciyar cudanya da Sauransu.

Ya kamata Iyaye da Al'umma da Malamai su kula sosai sannnan su dauki matakan dakile wannan mummunar Al'ada.

Allah Ya Sauwake, Ya karemu daga wannan Mummunar Al'ada.

Ku kasance da Shafin Ma'asumah Nigerian News Update don samun ingantaccen Labari, irinsu fadakar, nishadantarwa, wa'azantarwa da dai sauransu. sai kun zo.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post